Gwamnati Ta Fito da 'Barnar' Abubakar Malami a Kebbi, Ta Faɗi Yadda Tawagarsa Ta Riƙa Harbi
- Gwamnatin jihar Kebbi ta barranta kanta da harin da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ce an kai masa da tawagarsa
- Mashawarci na musamman ga gwamnan Kebbi kan yada labarai, Yahaya Sarki ya bayyana cewa mutanen Malami ne su ka fara neman husuma
- Ya jaddada cewa suna da hujjoji da shaidun da ke tabbatar da cewa ba 'yan APC ne su ka takali Malami ba, hasali ma kare kansu su ka yi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Gwamnatin jihar Kebbi ta karyata ikirarin jigo a jam'iyyar ADC, Abubakar Malami SAN da ya ce APC ta dauki nauyin kai masa da tawagarsa hari.
Wannan na biyo bayan zargin da Malami ya yi cewa jam'iyyar APC ta yi amfani da ƴan bangar siyasa wajen kai wa tawagarsa hari.

Source: Facebook
A wata sanarwa da Mashawarci na Musamman ga Gwamnan Kebbi, Yahaya Sarki, ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa APC jam'iyya ce da ke tsaftatacciyar siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta tsame kanta daga harin Malami
A tattaunawarsa da Legit, Yahaya Sarki ya ce hujjojin da ke hannunsu za su tabbatar da cewa Malami da mutanensa ne suka fara neman tayar da husuma.
Ya ce sun karya alluna dauke da hotunan Gwamna Nasir Idris da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a hanyarsu, wanda ke nuna cewa ba da zaman lafiya su ka je ba.
Yahaya Sarki ya ce:
""Wannan zargi ne da su 'yan ADC suka yi tare da Shugabansu, Malami. Su suka fara jan wannan fitina ko kai wa 'yan APC farmaki. Muna da shaidun abubuwan da suka faru tun suna bisa hanya."
"Hanyoyin da suka biyo, sun fara da kakkarya fastoci da alluna na APC wanda ke dauke da hotunan Shugaban kasa Tinubu da Gwamnan jihar Kebbi, Kwamred Nasir Idris Kauran Gwandu."
"Kuma baya ga haka, sun zo domin kara jan fitina, suka bi hannu daya, kusa da ofishin hedkwatarjam'iyyarmu ta APC. Muna da shaidu da ke nuna cewa har harbi suka yi da bindiga kuma sun fito da miyagun makamai."
Malami ya ba gwamnatin Kebbi mamaki
Yahaya ya bayyana mamakinsa a kan yadda Abubakar Malami SAN ya samu kansa a cikin hatsaniya da 'yan daba, lamarin da ya ce zai iya jawo matsaloli.
Ya ce:
"Tsohon Minista ne na Shari'a amma sai ga shi yanzu ya samu kan shi a gaba gaba, yana jagorancin bata gari na tada zaune tsaye a harkar siyasa."

Source: Facebook
"To gaskiya muna Allah wadai da wannan dabi'a ta 'yan ADC da kuma Shugabansu, Abubakar Malami SAN."
"Mun san yan aneman kujera amma ya kamata ya san hanyoyi na dimokuradiyya na neman wannan kujera ba ta hanyar tada zaune tsaye ba.
Ya ce kowa ya san 'yan APC na tsaftacciyar siyasa a jihar. Ya shawarci 'yan APC da sauran mazauna jihar da su tabbata sun zauna lafiya, inda ya ce yanzu haka bafun na gaban 'yan sanda.
Malami ya ce an kai masa hari a Kebbi

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta
A wani labarin, mun wallafa cewa Abubakar Malami, tsohon Minista a gwamnattin Muhammadu Buhari ya bayyana yadda ‘yan daba suka kai masa farmaki a jihar Kebbi.
Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malam SAN ya zargi jam'iyya mai mulki a jihar da daukar nauyin 'yan ta'addan da suka kai masu harin a hanyarsa ta dawowa daga fadar sarki.
Tuni APC ta yi martani, tare da bayyana cewa rundunar 'yan sandan jihar ta tsawatar a kan kokarin tayar da rikici, da kuma jan kunnen cewa yanzu ba kakar zabe ba ce.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

