2027: Matasa Za Su Haɗa Kuɗi, a Saya wa Gwamna Fom ɗin Takarar Shugaban Ƙasa

2027: Matasa Za Su Haɗa Kuɗi, a Saya wa Gwamna Fom ɗin Takarar Shugaban Ƙasa

  • Wata kungiyar matasa ta ce za ta saya wa Gwamna Seyi Makinde fom din tsaya wa takarar shugaban kasar Najeriya a 2027
  • Matasan sun bayyana cewa Makinde ne kawai dan siyasar PDP da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu da APC a zabe
  • Kungiyar ta ce ba za ta takura wa 'yan Najeriya ba, yayin da ta bayyana yadda za ta hada miliyoyin Naira don sayen fom din

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Wata ƙungiyar matasa ta NYAG-Makinde 2027, ta sanar da shirin ta na sayen fom ɗin takarar shugaban ƙasa ga Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a zaɓen 2027.

Wannan sanarwa ta fito ne a Bauchi a ranar Litinin, inda kungiyar ta bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne bayan jam’iyyar PDP ta kai takarar shugaban kasa yankin Kudu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tsagin Wike ya kafa sharuddan samun sulhu a jam'iyyar

Wata kungiyar matasan PDP ta sha alwashin hada kudi tare da saya wa Gwamna Seyi Makinde fom din takarar shugaban kasa
Gwamna Seyi Makide tare da wasu gwamnonin PDP a taron da suka gudanar a Zamfara. Hoto: @seyiamakinde
Source: Twitter

'Gwamna Makinde ne mafi dacewa ga PDP' - Kungiya

Da yake jawabi a madadin kungiyar, jaridar The Guardian ta rahoto Hon Lawal Abdullahi ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Seyi Makinde ne ya fi cancanta a zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, shi kadai ne dan siyasa daga Kudancin Najeriya da zai iya kayar da shugaba Bola Tinubu.”

Ya kara da cewa,

"Seyi Makinde yana da karfin da zai iya samun goyon baya daga Kudu maso Yamma da sauran yankuna, musamman Arewa, wadda ke kullace da gwamnatin APC."

Makinde: Matasa sun fara yakin neman zabe

Abdullahi ya bayyana cewa tun kafin sanarwar PDP, kungiyarsu ta fara gangamin neman takarar Makinde a matsayin shugaban kasa.

Ya tuna yadda suka sanya hotunan Makinde a faɗin jihohin Arewa 19 da kuma birnin tarayya Abuja, inda suke kira ga gwamnan da ya fito ya amsa kiransu.

Kara karanta wannan

2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara

Ya ce:

“Za ku tuna cewa watannin da suka gabata, mun bi jihohin Arewa 19 da Abuja, muna manna hotuna masu kira ga Seyi Makinde da ya fito takarar shugaban kasa a 2027."
Kungiyar matasa ta ce Gwamna Seyi Makinde ne kawai dan siyasar PDP da zai iya kayar da Tinubu a 2027
Gwamna Seyi Makinde yana latsa kamfuta a dakin taron gwamnonin PDP da suka gudanar a Zamfara. Hoto: @seyiamakinde
Source: Twitter

Yadda matasan za su hada kudin fom

Jaridar Daily Post ta rahoto Abdullahi ya kara da cewa yanzu da PDP ta kai takara Kudu, za su kara kaimi wajen tattara kuɗi domin sayen fom ɗin takarar ba tare da dora wa 'yan Najeriya wani nauyi ba.

“Da yake an ware tikitin shugaban kasa zuwa Kudu, aikinmu ya zo da sauƙi. Yanzu kawai za mu kara kaimi ne wajen hada kan ‘yan Najeriya masu irin wannan ra'ayin namu.
"Za mu tara kuɗi da za mu saya wa Gwamna Seyi Makinde fom din nuna sha'awa da kuma na tsaya wa takara, ba tare da mun mika kokon bara ga 'yan kasar ba."

- Hon Lawal Abdullahi.

Yiwuwar takarar Makinde da Gwamna Bala

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya fafata da Tinubu ba a 2027'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce akwai yiwuwar ya zama abokin takarar gwamnan Oyo, Seyi Makinde a zaben 2027.

Gwamna Bala Mohammed ya ce matakin da PDP ta dauka na kai takarar shugaban kasa Kudu a 2027 shi ne abin da ya fi dacewa don ba jam'iyyar nasara a zaben mai zuwa.

Gwamnan ya jaddada cewa PDP ba za ta maimaita abin da APC ta yi a 2023 ba, domin za ta yi la’akari da tsarin raba iko da daidaiton addini da kuma yanki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com