"Ya Isa Haka": Wike Ya Kai Gwamna Bala Makura kan Rikicin Jam'iyyar PDP

"Ya Isa Haka": Wike Ya Kai Gwamna Bala Makura kan Rikicin Jam'iyyar PDP

  • Tsugunne ba ta kare ba kan rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa a.jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed bai ji dadin sharuddun da tsagin Nyesom Wike ya gindaya ga jam'iyyar ba
  • Ya nuna cewa lokaci ya yi da za su fito su nuna cewa babu wanda suke tsoro a jam'iyyar domin ka da a ruguza ta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Shugaban gwamnonin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya yi martani kan bukatar da Nyesom Wike ya gabatar.

Mai girma Gwamna Bala Mohammed ya ce jam’iyyar PDP ta gaji da masu tada rikici a cikinta.

Gwamna Bala ya yi wa Wike martani
Hoton ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @GovWike, @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan jerin sababbin sharuddan da tsagin Nyesom Wike ya gindaya ga PDP.

Kara karanta wannan

APC ta kare salon mulkin Tinubu yayin da shugabannin siyasa a Arewa ke koka wa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nyesom Wike ya kafa sharudda ga PDP

Tsagin na Wike dai ya kafa sharudda ga jam'iyyar PDP domin amincewa da babban taronta na kasa da ake shirin gudanarwa.

Sun bayyana cewa dole ne shugaban jam’iyyar na kasa ya ci gaba da kasancewa daga Arewa ta Tsakiya, bisa tsarin rabon mukamai na babban taron 2021.

Wane martani Gwamna Bala ya yi?

Sai dai a martanin da ya yi, Gwamna Bala Mohammed ya ce shugabannin PDP ba masu rauni ba ne, rahoton The Guardian ya tabbatar.

"Ba za mu ci gaba da yin shiru ba mu bar mutane su kai mu su baro mu ba."
“Shugaban jam’iyya na kasa ya yi magana sosai. Kwarewar shugabannin kwamitin babban taro ba abin da za a yi shakka a kai ba ne, domin sun taɓa gudanar da hakan a baya, kuma mun yi imani za su sake yin yadda ya dace."

Kara karanta wannan

2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara

"Muna tare da kwamitin gudanarwa na kasa. Mun yaba da sadaukarwar da suke yi. Amma lokaci ya yi da dole mu nuna karfinmu. Mu ba masu rauni ba ne, ba mu jin tsoron kowa."
"Ba za mu ci gaba da yin shiru ba mu bar mutane su kai mu su baro mu ba. Aikin su kenan, amma namu aikin shi ne tabbatar da cewa hakan bai faru ba."
"Mu a matsayinmu na gwamnoni da kwamitin gudanarwa na kasa muna aiki domin mu tabbatar kalmar da ta fi muhimmanci ita ce ladabi da biyayya."
"Ba za mu kara bari ko mu yarda wani ya ɗauke mu da wasa ba. Dole hakan ya tsaya. Mun gaji da hakan. Ba za mu kara jurewa ba."

- Gwamna Bala Mohammed

Gwamna Bala ya caccaki Wike
Hoton gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Gwamna Bala ya hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya hakura da takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Gwamna Bala ya bayyana cewa zai yi biyayya ga matakin da jam'iyyar ta dauka na kai tikitin takararta zuwa yankin Kudancin Najeriya.

Ya bayyana cewa ya hakura da burinsa na yin takarar ne domin ci gaban jam'iyyar da hadin kai a fadin kasa gaba daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng