Rikicin PDP: Tsagin Wike Ya Kafa Sharuddan Samun Sulhu a Jam'iyyar
- Ana ci gaba da kai kawo kan rikicin cikin gida da yana addabar babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya watau PDP
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da mutanensa sun gindaya sharuddan samun zaman lafiya
- Sun bayyana cewa idan ana son zaman lafiya a PDP dole ne a yi abubuwan da suke so a jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata kungiyar PDP mai suna 'Eminent Elders and Concerned Stakeholders' karkashin jagorancin Nyesom Wike, ta kafa sharudda ga jam'iyyar.
Kungiyar ta nemi a takaita takarar kujerar shugaban jam’iyyar PDP na kasa a yankin Arewa ta Tsakiya kawai.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan taron da ta gudanar a daren ranar Litinin a Abuja, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta Wike ta gindaya wasu sharudda da take son a bi, kafin su amince da babban taron jam’iyyar na kasa da ake shirin gudanarwa.
Wadane sharudda tsagin Wike suka gindaya?
Kungiyar ta bukaci PDP ta gudanar da sabon zaɓen shugabannin jam’iyya a jihohin Ebonyi da Anambra, tare da amincewa da sakamakon zaben shugabannin yankin Kudu maso Kudu da aka gudanar a birnin Calabar, jihar Cross River.
Haka kuma ta nemi a gudanar da zaɓen shugabannin kananan hukumomi a jihar Ekiti cikin gaggawa, domin bin umarnin kotu, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
"Mun amince da shawarwarin kwamitin rabon mukamai da NEC ta amince da shi, inda aka ce a bar tsarin mukaman jam'iyya yadda su ke."
"Amma muna kara jaddada cewa babu bukatar yin karin rabon cikin gida domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jam’iyya."
"Saboda haka, dole ne shugaban jam’iyya na kasa ya kasance daga Arewa ta Tsakiya, bisa tsarin rabon mukamai na babban taron jam’iyya na 2021."
Tsagin Wike ya gargadi shugabannin PDP
Kungiyar ta yi gargadi cewa rashin bin waɗannan sharudda zai sanya babban taron ya kasance mara inganci.
Ta bayyana cewa taron zai kasance mara inganci saboda za a hana sahihan mambobin jam’iyya ‘yancinsu.

Source: Twitter
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Nyesom Wike, Samuel Anyanwu (sakataren jam’iyyar PDP na kasa), tsofaffin gwamnonin jihohi, Okezie Ikpeazu (Abia), Samuel Ortom (Benue), Ayo Fayose (Ekiti).
Sauran sun hada da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Kingsley Chinda (shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai), Martins Ameawhule (shugaban majalisar dokokin jihar Rivers da aka dakatar), da sauransu.
Wike ya ba Goodluck Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba da shawara ga Goodluck Jonathan, kan batun yin takara.
Nyesom Wike ya bukaci tsohon shugaban kasan da ka da ya bari a yaudare shi ya fafata da mai girma Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.
Ministan ya bayyana cewa yana da kyau Jonathan ya ci gaba da rike mutuncin da yake da shi maimakon dawowa siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

