'Yan Majalisa da 'Yan Siyasa da Suka Rasu ba a Jima da Rantsar da Su ba

'Yan Majalisa da 'Yan Siyasa da Suka Rasu ba a Jima da Rantsar da Su ba

  • Najeriya ta yi jimamin mutuwar wasu zababbun shugabanni da suka riga mu gidan gaskiya makonni kaɗan bayan rantsar da su
  • Daga Hon. Akinremi na Ibadan ta Arewa, zuwa Oluwakemi Rufai a Ibeju-Lekki da Zainab Shotayo, an yi rashin 'yan siyasa
  • Wannan mutuwar kwatsam ta sa al’umma tunani kan matsalolin lafiya, tasirin siyasa, da gajeriyar rayuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kwanan nan, Najeriya ta yi jimamin mutuwar wasu zababbun shugabanni da suka riga mu gidan gaskiya cikin makonni kaɗan da suka hau mulki bayan rantsuwa.

Wannan rashi kwatsam ya tayar da hankula kan lafiyarsu, dawarniyar siyasa da aikin hidima ga al’umma duba da shekarunsu

Yan majalisu da suka bar duniya jima kadan bayan shiga ofis
Mutuwar wasu yan majalisa yar bazata ya ta da hankulan jama'arsu. Hoto: OduwoleShuwa/X.
Source: Twitter

'Yan siyasar da suka mutu bayan rantsar da su

Rahoton Tribune ta tabbatar da mutuwar inda aka bayyana irin gudunawar da suka bayar kafin rasuwarsu wanda ya kawo ci gaban al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fadi yankin da ya fi more ayyukanta na alheri

Rasuwar ta su kwatsam ta nuna tasirin rayuwa da rashin tabbas a cikin hidimar jama’a, inda jama’a ke jimami da tunani kan gajeriyar rayuwar da suka yi.

Rashin nasu ya zo a daida lokacin da aka fi bukatar su duba da cewa yawancinsu matasa ne.

Ga jerin zababbun wakilai na Najeriya da suka mutu bayan rantsar da su, bisa rahotanni da hukumomin da aka tabbatar da sahihancinsu.

1. Ibadan ta Arewa: Hon. Olaide Adewale Akinremi

'Dan majalisar wakilai na Ibadan ta Arewa, Hon. Olaide Adewale Akinremi ya yi bankwana da duniya.

'Dan majalisar wakilan wanda aka fi sani da “Jagaban,” ya riga mu gidan gaskiya bayan rantsar da shi.

Marigayin wanda aka sake zaɓensa a 2023 an rantsar da shi a watan Yuni 2023, amma abin takaici ya riga mu gidan gaskiya a ranar 10 ga Yuli 2024.

Mutuwarsa ta girgiza abokan aiki da mazabarsa, inda mutane da dama suka bayyana shi a matsayin ɗan majalisa mai kishin ƙasa da kusanci da jama’a.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin NEMA, Ambaliya ta afka wa dubban mutane a Adamawa

Akinremi ya kasance fitacce a siyasar jihar Oyo, inda ya yi suna wajen kare matasa da kuma ci gaban ayyukan gine-gine da raya kasa.

Dan majalisar tarayya ya rasu a Oyo
Marigayi dan majalisar tarayya, Musiliu Olaide Akinremi. Hoto: @mrlurvy.
Source: Twitter

2. Lekki, Lagos: Oluwakemi Rufai

'Yar majalisar yankin C1 a Ibeju-Lekki ta Lagos, Oluwakemi Rufai ta rasu bayan makonni biyu kacal da nasarar lashe kujerarta.

Ita ce kaɗai mace da aka rantsar a majalisar dokokin Ibeju-Lekki, inda aka tabbatar ta rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

Mai magana da yawun APC a Lagos, Seye Oladejo, ya bayyana Rufai a matsayin “ƙwararriya matashiya, mai kishin jam’iyya da hidima ga jama’a.”

Ya ce a dan zamanta a majalisar, Oluwakemi Rufai ta nuna biyayya ga jam’iyya da kuma kishin ci gaban al’umma ta hanyar wakilci mai inganci.

Rasuwarta ta yi matuƙar ta da hanakali, ganin rawar da take takawa a matsayin mai wakilcin al'umma musamman mata a harkokin mulki na yankin Ibeju-Lekki.

Kansila ta mutu bayan rantsar da ita a Lagos
Marigayiya Oluwakemi Rufai kenan kafin rasuwarta. Hoto: @horiiyomi.
Source: Twitter

3. Odi-Olowo/Ojuwoye: Zainab Shotayo

Har ila yau, yar majalisar Odi-Olowo/Ojuwoye, Zainab Shotayo ta riga mu gidan gaskiya bayan rantsar da ita.

Marigayiywar ta rasu a ranar 18 ga watan Agustan 2025, abin da ya jefa majalisa cikin alhini, Punch ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Yan bindiga sun yashe gari tas, sun sace basarake da duka limaman gari

An gudanar da zaman musamman a majalisa domin tunawa da ita, inda aka yaba mata a matsayin wakiliya mai kishin jama’arta.

Shugaban karamar hukumar, Seyi Jakande, ya bayyana ta a matsayin mai himma da jajircewa wajen warware matsalolin al’umma da inganta mulki.

Mutuwarta ta ƙara nuna yadda Ubangiji ke dauke wasu ‘yan siyasa da suka sadaukar da kai wajen hidimar jama’a amma suka samu katsawar rayuwa.

Rasuwar Akinremi, Rufai da Shotayo ta sa mutane na tunani kan tasirin kalubalen siyasa da muhimmancin lafiyar shugabanni a Najeriya.

Kansila ta mutu bayan rantsar da ita a Lagos
Hon. Zainab Shotayo yayin wani taro a Lagos. Hoto: Awofisayo Yetunde Victoria.
Source: Facebook

'Dan majalisa ya mutu a Oyo

Kun ji cewa an tabbatar da rasuwar tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin jihar Oyo kuma babban jigo a jam'iyyar APC, Hon. Kehinde Subair.

Tsohon ɗan Majalisar Dokokin ya riga mu gidan gaskiya ne a Birtaniya ranar Juma'a, 13 ga watan Maris, mako guda kafin ya gudanar da bikin cika shekaru 60.

Sanata mai wakiltar Oyo ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Yunus Akintunde ya yi alhinin rashin tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.