Bayan Ribadu da Uba Sani Sun Yi Raddi, Sanata Shehu Sani Ya Duro kan El Rufa'i
- Sanata Shehu Sani ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, bai taɓa taka rawa a fafutukar kare dimokraɗiyya ba
- Kalamansa na zuwa ne bayan manyan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da wasu 'yan APC sun sako El-Rufai a gaba saboda kalamansa
- Malam El-Rufai ya jawo magana ne bayan ya wata hira da ya yi a makon nan, inda ya fi fata-fata da mulkin Bola Ahmed Tinubu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, bai yi wani tasiri a fafutukar demokraɗiyyar Najeriya ba.
Sanata Shehu Sani ya yi wannan magana ne a yayin da ake ce-ce-ku-ce a tsakanin El-Rufai da gwamnatin jihar Kaduna kan rikicin da ya ɓarke yayin taron 'yan adawa.

Source: Facebook
A hirarsa da Channels Television, El-Rufai ya ce ba shi buƙatar izinin ‘yan sanda domin yin taro, tare da zargin gwamnatin jihar Kaduna da hannu a kai masu farmaki.
Gwamnati da El-Rufai suna zargin juna
Jaridar Punch ta ruwaito cewa sai dai gwamnatin Kaduna ta musanta zargin, inda ta ce El-Rufai na ƙoƙarin tayar da hankalin jama’a ta hanyar rudi, yaudara da karya.
Kwamishinan tsaro na cikin gida, Suleiman Shuaibu ya fitar da sanarwa, inda gwamnati ta ce taron siyasar da El-Rufai ya shirya a ranar 30 ga Agusta, haramtacce ne.
Taron kalaman Nasir El-Rufai sun jawo raddi daga bangarori da dama, daga ciki har da Mashawarcin Shugaban Kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
A martani ga zargin biyan 'yan ta'adda alawus, Ribadu ya ce:
“Babu wani lokaci da ONSA ko wata hukuma a karkashin wannan gwamnati ta taba shiga yarjejeniya ta biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda. Kishiyar haka mu ka yi, domin mun rika gargadin jama’a da su guji biyan kudin fansa.”
Sanata Shehu Sani ya dura kan El-Rufai
Da yake magana a kan dambarwar, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa shi ya shiga harkar gwamnati ne ta dalilin gwagwarmaya da sadaukarwa.
Ya ce ba kamar El-Rufai ba, ya sha gwagwarmaya da ta kai ga ɗaurin kurkuku a lokutan mulkin soja.

Source: Twitter
Ya ce:
“Ni na san da ƙyar na tsira a rayuwata. Na sha zama a kurkuku da ofisoshin ‘yan sanda da ɗaurei da sarka a ƙafa da ankwa a hannu a matsayin ɗan fafutuka.”
Sani ya ƙara da cewa shi ya fito ne daga fagen gwagwarmaya, yayin da El-Rufai ya samu shahara ne bayan 1999 ta hanyar mukaman gwamnati da siyasa.
Ya ce mutane irin Nasir El-Rufai sun tsinci dami a kala ne a magana ta siyasa, domin bai tabuka mata wani abin a zo a gani ba.
Wike ya kalubalanci El-Rufai
A baya, mun wallafa cewa Ministan Babban Birnin Tarayya (Abuja), Nyesom Wike, ya maida martani ga hasashen tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai kan zaben 2027.

Kara karanta wannan
'Kalamanka na da haɗari,' CAN ta taso El Rufai a gaba kan yawan Kiristocin Kaduna
El-Rufai ya yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC za su fuskanci kalubale mai tsanani a zabe mai zuwa, har ma ya yi hasashen cewa za su fadi zabe.
Sai dai a hirar da Wike ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025, ya ce babu wani tushe a cikin maganganun tsohon gwamnan Kaduna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

