2027: Sanata Marafa Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu Bayan Manufofinsa a Arewa

2027: Sanata Marafa Ya Yi Hasashen Makomar Tinubu Bayan Manufofinsa a Arewa

  • Sanata Kabiru Garba Marafa na jihar Zamfara ya yi gargadi a kan makomar Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Ya yi gargadin cewa Shugaba Tinubu zai iya fuskantar ƙalubale wajen samun ƙuri’un Arewa a zaɓen 2027
  • Sanata Marafa ya zargi gwamnati da kin baiwa Arewa muhimmanci wajen ayyuka da wakilci a gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara– Sanata Kabiru Garba Marafa, tsohon daraktan yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu a Zamfara a 2023 ya ce akwai matsala a 2027.

Ya ce akwai barazanar Shugaban Ƙasa zai rasa goyon bayan yawancin ‘yan Arewa a 2027 idan abubuwan da ake gani yanzu ba su sauya ba.

Marafa ya caccaki Bola Ahmed Tinubu
Sanata Kabiru Garba Karafa/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Garba Marafa/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa Marafa ya ce ya fice daga APC saboda abin da ya kira watsi da su da jama'ar Arewa Bola Ahmed Tinubu ya yi tun bayan hawa mulki.

Kara karanta wannan

Shugaban yakin zaben Tinubu ya juya baya, ya yi wa APC barazanar faduwa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marafa ya soki Tinubu

Marafa ya kara da cewa dangantakar shugaban ƙasa da Arewa ta yi rauni sosai musamman saboda yadda gwamnati ke raba ayyuka.

Ya lissafa tabarbarewar tsaro, gaza kammala manyan ayyuka, da kuma watsi da fitattun shugabanni a yankin a matsayin dalilan rashin jin daɗin jama’a.

Marafa wanda a baya ake ganin babban abokin Tinubu ne a Arewa maso Yamma, ya ce APC na cikin haɗari.

Ya ce:

“A cikin shekaru biyu, ban ga wani babban aiki da aka kammala wa Arewa ba. Ka ɗauki hanyar Abuja–Kano, har yanzu tana nan cak. Amma duba kuɗin da aka kashe a Lagos kaɗai."

Martanin gwamnatin tarayya ga Marafa

Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa an raba ayyukan gwamnati a shiyyoyin kasar nan.

Ya kuma ce babu wani wariya wajen naɗe-naɗen gwamnati, domin shugaban ƙasa ya nuna ƙwarewa a jagorancinsa.

Sai dai Marafa ya dage cewa gwamnatin Tinubu tana muzgunawa shugabanni a Arewacin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: El Rufa'i ya yi wa Ribadu da Uba Sani wankin babban bargo

Marafa ya ce Arewa na fushi da Tinubu
Hoton Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya yi misali da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, inda ya ce duk da amincinsu a lokacin zaɓe, an tura su gefe bayan kammala yaƙin neman zaɓe kuma an samu nasara.

Marafa ya ƙara da cewa ko da yake Tinubu mutum ne da ba ya nuna wariya, amma gwamnatin sa ta kasa tabbatar da adalci ga Arewa wajen rabon ayyuka da damar cigaba.

Marafa ya juya wa Tinubu baya

A wani labarin, mun wallafa cewa APC ta samu matsala da tsohon Sanata kuma jigon jam’iyyar, Kabiru Garba Marafa, wanda ya yi jagorancin yakin neman zabenta a 2023.

Sanata Marafa, shi ne ya wuce gaba a wajen yakin Bola Tinubu da Kashim Shettima a shekarar 2023, ya sha alwashin rage wa Tinubu kuri’u miliyan ɗaya a 2027.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa barinsa daga jam’iyyar ya biyo bayan rashin jin daɗinsa da salon siyasar Tinubu, inda ya zargi shugaban ƙasa da “amfani da mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng