Shugaban Yakin Zaben Tinubu Ya Juya Baya, Ya Yi wa APC Barazanar Faduwa a 2027

Shugaban Yakin Zaben Tinubu Ya Juya Baya, Ya Yi wa APC Barazanar Faduwa a 2027

  • Sanata Kabiru Marafa ya ce zai cire kuri’u miliyan daya daga cikin wadanda Bola Tinubu zai samu a zaben 2027
  • Marafa ya bayyana hakan ne bayan ficewarsa daga APC, inda ya zargi shugaba Tinubu da watsi da mutane
  • Tsohon Sanata ne shugaban yakin neman zaben Bola Tinubu da Sanata Kashim Shettima a shekarar 2023 a Zamfara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon Sanatan Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Garba Marafa, ya sha alwashin rage wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’u miliyan 1 daga cikin na shi a zaben shekarar 2027.

Sanata Kabiru Marafa ya taba kasancewa jigo a jam’iyyar APC mai mulki kafin ya sanar da sauya sheka ya koma adawa.

Sanata Marafa da shugaba Bola Tinubu
Sanata Marafa da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Kabiru Garba Marafa|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit Hausa ta rahoto cewa ya sanar da hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a wani shiri na tashar Channels Television a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2027: Sanata Marafa ya yi hasashen makomar Tinubu bayan manufofinsa a Arewa

Ya ce matakin nasa ya samo asali ne daga rashin jin dadinsa da irin salon siyasar Tinubu, wanda ya zarge shi da amfani da mutane a lokacin bukata sannan daga baya a jefar da su.

Marafa zai rage wa Tinubu kuri’u miliyan 1

Sanata Marafa ya bayyana cewa zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da rage kuri’u miliyan 1 daga wadanda Shugaba Tinubu zai iya samu a 2027.

Jaridar Tribune ta rahoto ya kara da cewa:

“Ina tabbatar muku yau. Zan cire kuri’u miliyan 1 daga cikin na shugaban kasa, na yi niyya kuma da yardar Allah zan yi nasara.”

Ya ce masu kiran shi da dan siyasa marar tasiri za su gane gaskiya a zaben 2027, domin shi ya yi niyyar tabbatar da tasirin sa a siyasar Zamfara da Najeriya baki daya.

Dalilan ficewar Sanata Marafa daga APC

Tsohon Sanatan ya bayyana cewa ana halin rashin jin dadi daga jama’ar gari zuwa manyan ‘yan siyasa a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Siyasa ta fara tsami: An farmaki ministan Buhari a Kebbi, APC ta ɗauki zafi kan lamarin

A cewarsa, kusan dukkan ‘yan siyasa masu tasiri a jihar sun hade a gefe guda, amma duk da haka an sha kaye a zaben gwamna da aka yi a 2023, inda Dauda Lawal na PDP ya yi nasara.

Ya ce nasarar Tinubu a Zamfara a wancan lokaci ta samo asali ne daga sakon da aka rika bai wa jama’a cewa zai sauya tsarin APC, sakamakon korafe-korafe a karshen mulkin Buhari.

Sai dai a cewarsa, ba a ga wani sauyi ba, kuma hakan ne ya sanya shi daukar matakin fita daga APC zuwa adawa.

Shugaba Bola Tinubu yayin taro a kasar waje
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a kasar waje. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Marafa ya zargi Tinubu da cin amana

Marafa ya yi zargin cewa Shugaba Tinubu bai cika alkawarin da ya dauka ba na kawar da tsarin wadanda suka sha wa jam'iyya wahala.

Ya ce maimakon hakan, Tinubu ya kara karfafa tsarin a APC, ya kuma mayar da shi al’ada da manufofin jam’iyyar.

A cewar Marafa, hakan ne ya kara haifar da rashin jin dadi daga jama’a da kuma rasa goyon bayan da ake bukata daga wadanda suka yi amfani da karfin su wajen goyon bayan Tinubu.

Tinubu ya ce yana kokari a Najeriya

Kara karanta wannan

"Mayunwata ne": Hadimin Tinubu ya caccaki El Rufai da masu son kifar da shugaban kasa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yana kokari ba tare da nuna wariya ba.

Bola Tinubu ya tabbatar da cewa yana adalci kamar yadda ya yi rantsuwa a 2023 cewa zai yi wa kowa adalci.

Shugaban kasar ya yi magana ne bayan an yawaita zarge zarge kan cewa yana fifita jihar Legas da ya fito wajen manyan ayyuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng