Siyasa Ta Fara Tsami: An Farmaki Ministan Buhari a Kebbi, APC Ta Ɗauki Zafi kan Lamarin

Siyasa Ta Fara Tsami: An Farmaki Ministan Buhari a Kebbi, APC Ta Ɗauki Zafi kan Lamarin

  • A ranar Litinin, wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai hari kan jerin motocin tsohon minista a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari
  • Majiyoyi sun ce tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami ya gamu da fushin matasa a Birnin Kebbi
  • Abubakar Malami SAN ya zargi yan APC inda ya ce ya je gaisuwar mutuwa ne ba sha'anin siyasa ta kai shi ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Kebbi, Kebbi - Ana zargin wasu yan daba sun kai hari kan tsohon minista a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

A yau Litinin, wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan jerin motocin jigo jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi, Abubakar Malami.

Yan daba sun farmaki tsohon minista
Tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Abubakar Malami. Hoto: Abubakar Malami.
Source: Facebook

Rahoton Punch ya ce lamarin ya faru ne jim kadan bayan dawowar Malami jihar, inda ya je ziyarar ta’aziyya ga wasu iyalai da suka rasa masoyansu.

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin barin Malami APC zuwa ADC

Hakan na zuwa ne wata biyu kacal bayan tsohon ministan ya bar jam'iyyar APC zuwa ADC mai adawa a Najeriya.

Malami na daga cikin jerin ministoci a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari daga 2015 har zuwa shekarar 2023 da suka bar mulki.

Malami ya zargi APC da kai masa hari

Shaidu sun bayyana cewa akalla motoci 10 aka lalata, sannan magoya bayansa da dama sun samu raunuka daban-daban sakamakon harin da aka kai.

Malami wanda ya rike Ministan Shari’a daga 2015 zuwa 2023 ya bayyana harin da cewa yana da alaka da siyasa.

Ya ce:

"Na je Birnin Kebbi musamman domin ziyarar ta'aziyya ga wasu iyalai da suka rasa masoyansu ba maganar siyasa ba ce ta kawo ni.
“Akwai daci kuma abin takaici, wasu ’yan daba daga hedkwatar APC sun fito dauke da makamai da duwatsu, suka kai mana hari.

Kara karanta wannan

Siyasar Sanatan APC da ministan Tinubu na fuskantar matsala, an bukaci su ja baya

“Sun lalata motocinmu kuma sun raunata magoya bayanmu. Amma idan aka zo batun siyasa a Kebbi, babu ja da baya."
Ana zargin yan APC da kai farmaki kan ministan Buhari
Tsohon ministan Shari'a, Abubakar Malami lokacin da yake ofis. Hoto: Abubakar Malami, SAN.
Source: Depositphotos

APC ta yi martani kan zargin Malami

Sai dai jam’iyyar APC a Kebbi ta musanta hannu a lamarin, inda kakakin yada labaranta, Isa Assalafy, ya nesanta jam’iyyar daga harin, Channels TV ta ruwaito.

Ya ce:

"Babu gwamnatin da ke samun goyon bayan al'ummarta da hasken nasara a zaben 2027 da za ta kawo cikas a zaman lafiya."

Assalafy ya kara da cewa jami’an tsaron da ke tare da Malami sun bude wuta a lokacin rikicin, wanda hakan ya sa lamarin ya ta’azzara.

Sai dai rundunar ’yan sandan Kebbi ba ta fitar da sanarwa a hukumance game da harin ba, har zuwa lokacin tattara wannan rahoton.

Tsohon minista ya caccaki Tinubu, APC

Kun ji cewa tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya soki jam’iyyar APC bisa nuna goyon baya ga Bola Tinubu a 2027 duk da halin da kasa ke ciki.

Malami ya ce gwamnati ta fi maida hankali kan siyasa maimakon warware matsalolin da ke damun talakawa musamman a Arewa.

Ya yi magana ne yayin da wasu 'yan siyasa a Arewa suka cimma matsaya kan hada kai don samun madafa mai ƙarfi a siyasar Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.