2027: Wike Ya Kyale Jonathan, Ya Fadi Mutum 1 da Zai Rusa PDP idan Ya Samu Takara

2027: Wike Ya Kyale Jonathan, Ya Fadi Mutum 1 da Zai Rusa PDP idan Ya Samu Takara

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce PDP za ta jefa kanta cikin halaka idan ta dawo da tsohon ɗan takarar jam'iyyar LP, Peter Obi
  • Nyesom Wike ya ce, akwai alamar har yanzu PDP ba ta koyi darasi daga kura-kuran da suka jawo mata faduwa a zaben 2023 ba
  • Ministan ya gargadi jam’iyyar cewa rashin daidaito da kin yarda da tsarin sauya mulki na iya ci gaba da raunana ta har zuwa 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya gargadi jam’iyyar PDP cewa zata iya rusa kanta gaba ɗaya idan ta yarda ta dawo da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi.

Wike ya bayyana haka ne a lokacin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa bai kamata Jonathan ya fafata da Tinubu ba a 2027'

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce dawo da Peter Obi cikin PDP zai rusa jam'iyyar a 2027.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, yana jawabi a wani taro a Abuja. Hoto: @OfficialFCTA
Source: Facebook

PDP ba ta koyi darasi ba inji Wike

A yayin tattaunawar, Wike ya sake jaddada cewa PDP ba ta koyi darasi daga kuskuren da ya jawo mata rashin nasara a zaben 2023 ba, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya tuna yadda ya shaidawa shugabannin PDP cewa haɗari ne, kuma rashin adalci a siyasa, a bar ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iyya duka daga Arewa.

Ya ce tun da farko ya yi gargadin cewa wannan matsaya za ta jawo illa, amma shugabannin jam’iyyar suka ki sauraronsa, abin da ya sa suka sha mummunan kayi a zaɓen da ya gabata.

'Dawo da Obi babban haɗari ne' - Wike

Tsohon gwamnan na Ribas ya ce PDP ta yi abin kunya wajen karkatar da kujerun ɗan takarar shugaban ƙasa da na shugaban jam’iyya, abin da ya kira da “sata biyu.”

A cewarsa, hakan ya jawo jam’iyyar ta rasa kwarjini kuma ta fuskanci abinda ya bayyana da “cikakkiyar azaba” a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Keyamo ya hango abin da zai faru idan Peter Obi ya koma PDP

Wike ya yi watsi da rade-radin cewa PDP na iya dawo da Peter Obi, yana mai cewa hakan babban haɗari ne ga makomar jam’iyyar.

Ya tambaya meya sa jam’iyyar za ta karɓi mutumin da ya rika zagin ta, yana cewa Obi ya kira PDP “jam’iyyar da ta lalace” amma yanzu ana tunanin dawo da shi saboda siyasa.

Wike ya ce kuskuren da PDP za ta tafka a 2027 shi ne dawo da Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, a cikin ofis dinsa. Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Wike ya kawo mafita ga jam'iyyar PDP

Ministan ya kara jaddada cewa babu yadda PDP za ta dawo da karfinta matuƙar ba ta rungumi adalci, sauya mulki da bin tsarin raba mukamai tsakanin Arewa da Kudu ba.

Ya ce wadannan su ne ginshikan da za su iya dawo da martabar jam’iyyar a siyasar Najeriya, kuma hakan ne kawai zai sa ta yi tasiri a zaben 2027.

2027: PDP ta fara zawarcin Peter Obi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu jiga jigan jam'iyyar adawa ta PDP, sun fara zawarcin tsohon dan takarar LP, Peter Obi, zuwa jam'iyyar gabanin 2027.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro ya bayyana cewa tuni jiga-jigan PDP suka fara sanya labule da Obi don ya dawo babbar jam'iyyar.

Baya ga Obi, Sanata Abba Moro ya kuma ce ana kan tattaunawa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, kan yiwuwar tsaya wa takara a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com