"Mayunwata ne": Hadimin Tinubu Ya Caccaki El Rufai da Masu Son Kifar da Shugaban Kasa
- Hadimin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi martani kan kalaman da Nasir El-Rufai ya yi kan gwamnatin ubangidansa
- Bayo Onanuga ya bayyana cewa tsohon gwamnan na Kaduna ya shiga cikin matsalar rudu a siyasa
- Mai taimakawa shugaban kasan ya lissafo wasu daga cikin nasarorin da Tinubu ya samu a shekara biyun da ya kwashe kan mulki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya caccaki Nasir El-Rufai da sauran masu son a raba mai girma Bola Tinubu da mulki.
Bayo Onanuga ya bayyana waɗanda ke kira da a raba Shugaba Tinubu da mulki a matsayin ’yan siyasa masu yunwar mulki.

Source: Twitter
Onanuga mai shekara 68 ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin na Shugaba Tinubu ya maida martani ne kan wata hira da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Me Hadimin Tinubu ya ce kan El-Rufai?
Onanuga ya zargi El-Rufai da kasancewa a sahun gaba na shirin ganin an raba Shugaba Tinubu da mulkin Najeriya.
Hadimin shugaban kasan ya ce El-Rufai yana jagorantar shirin duk da cewa ya taɓa amincewa a baya cewa shekara huɗu sun yi kadan ga kowane shugaba ya aiwatar da “canje-canjen da za su yi tasiri”.
"Nasir El-Rufai ya amince a nan cewa shekara huɗu sun yi kadan ga mai rike da mukamin siyasa wajen yin muhimman canje-canje."
"Amma yanzu shi ne a sahun gaba na gungun ’yan siyasa masu neman mulki ido rufe da ke shirya kifar da Shugaba Tinubu, shekara biyu kacal a kan mulki. Wane irin kwan gaba kwan baya ne wannan!"
"Sabanin waɗannan tsofaffin gwamnonin marasa kwarewa da karancin nasara na Anambra, Rivers, da Kaduna, Shugaba Tinubu da tawagarsa sun aiwatar da manyan sauye-sauye a kasarmu cikin shekaru biyu da suka gabata."
- Bayo Onanuga
Onanuga ya lissafo ayyukan Tinubu
Onanuga ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta samu manyan nasarori cikin shekaru biyu, inda ya kawo misalai da bunƙasar kasuwar hannun jari, daidaita tsarin musayar kuɗi, da kuma raguwar hauhawar farashin kaya. na tsawon watanni huɗu a jere.
Ya kuma nuna gyare-gyare a fannin ilimi da walwalar jama’a, ciki har da shirin ba da lamuni ga ɗalibai na NELFUND da kuma bayar da tallafin kuɗi ga gidajen talakawa masu rauni.
Haka kuma, ya ce jihohi da kananan hukumomi suna samun karin kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya, wanda hakan ya ba su damar gudanar da manyan ayyukan raya kasa da samar da ayyukan yi.

Source: Twitter
"Gwamnoni da kansu sun ce ba su taɓa samun irin wannan alheri ba."
"Amma wadannan 'yan siyasan masu yunwar mulki suna son a cire shugaban kasa wanda ya samu nasarori sosai, saboda kawai sun daina tasiri a siyasa. Ka da Allah ya ba su nasara a shirinsu kan kasarmu da mutanenta."
- Bayo Onanuga
Gwamnati ta musanta zargin El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya yi martani kan zargin da Nasir El-Rufai, ya yi.
Malam Nuhu Ribadu ya musanta zargin da El-Rufai ya yi na cewa gwamnatin tarayya na ba da kudade ga 'yan bindiga.
Hakazalika, ofishin ya bayyana zargin na El-Rufai a matsayin cin mutunci ga jami'an tsaro wadanda suka sadaukar da kansu wajen kare kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


