Zargin Badaƙalar N6.8bn: Ganduje Ya Nemi a fara Shirin Tsige Gwamna Abba a Kano
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kalaman da su ka tayar da kura a siyasar jihar bayan zargin rashawa a gwamnatin NNPP
- Ganduje ya ce bai kamata majalisar dokokin jihar ta yi gum ba, domin zargin cin hanci da rashawar da aka yi wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta girmama
- Tsohon Shugaban APC na kasa ya ce akwai bukatar a tuhumi Abba Kabir, sannan a dauki matakin shari'a a kansa idan zargi ya tabbata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya jawo magana bayan wasu kalamai da ya yi a kan zargin cin hanci da rashawa da gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Bayaninsa na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta wanke Daraktan kula da harkokin gidan gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo, daga zargin cewa ya karkatar da N6.8bn daga asusun jihar.

Source: Facebook
A wani bidiyo mai daƙiƙa 47 da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, ana iya jin muryar Ganduje inda yake neman a tsige gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin Ganduje a kan gwamnatin Abba
A kalamansa a madadin Abdullahi Umar Ganduje, fitaccen ɗan siyasa a Kano, Mujahid Zaitawa ya ta cikin wani bidiyo a shafin Facebook ya akwai badakaloli a gwamnatin Abba.
Ya bayyana cewa shi (Zaitawa) ne ya jagoranci bankado badakala kala-kala a gwamnatin Kano, har ta kai aka fito da bayanai a idon duniya.
A kalaman Zaitawa:
“Badakala da cin hanci da rashawa ta baibaye gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf. Dalilai a nan mabayyana ne. Na farko dai, ni ne na jagoranci rubuta korafi a kan balahira da badakala na hakkinku mutanen Kano na shinkafa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba ku talakawa.”
Wannan ne ya sa suka miƙa koke ga hukumar cin hanci da rashawa da hukumar da’ar ma’aikata, har ta kai gwamna ya ɗauki matakin sauya masa ofis.
Zaitawa ya ce:
“Na kuma jagoranci badakalar NOVEMED, wacce ake ɗaukar N10m a asusun talakawan jihar Kano na kananan hukumomi 44.”
Ya ce bayan an gudanar da bincike ne aka gano irin barnar da ya ce an yi a asusun kananan hukumomin jihar Kano, kuma sun shafe akalla watanni shida suna ci gaba da bincike.
Abba: Sakon Ganduje ga majalisar Kano
Da yake ci gaba da magana a madadin Ganduje, Zaitawa ya ce akwai abin kunya a yadda ake samun badakala a gwamnatin Abba Kabir Yusuf duk da rantsuwar da ya yi da Alkur’ani mai tsarki.
Ya yi karin bayani a kan kalaman Ganduje na majalisar dokokin jihar Kano ta gaggauta tsige Abba, a bincike shi, sannan a tura shi gidan yari saboda badakala a gwamnatinsa.

Source: UGC
Ya ce:
“Ya ce kamata ya yi majalisar dokokin Kano ta tumbuke gwamna, domin gazawarsa a kan yaƙi da cin hanci da rashawa da yake ba a masa suna. Ana amfani da gwamnatinsa a wajen bata wa Abdullahi Umar Ganduje suna.”
“In har gwamna zai fito ya faɗi cewa amana ta yi ƙaranci babu babba babu yaro, ai gazawarsa ta tabbata, ba zai iya ba.”
Mujahid ya yi zargin cewa gwamnan Kano yana ɗaukar kalaman masu zuga shi wajen ƙoƙarin tuhumar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da ta shuɗe, kuma hakan, a cewarsa, ba daidai ba ne.
Abba zai binciki badakala a gwamnatin Ganduje
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti domin binciken yadda aka sayar da katafaren wurin yankar dabbobi na Kano da aka fi sani da Abatuwa,
An samar da mayankar wacce darajarta ta kai ta miliyoyin Naira a zamanin tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso domin samar da kudin shiga da kuma ayyukan yi ga jama’a.
Gwamna Abba ya sha alwashin zakulo yadda tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sayar da wannan katafaren wuri, kuma ba zai bar dukiyar jama'a ta salwanta ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


