'Ba don Addini ba ne,' El Rufa'i Ya Fadi Dalilin Kawo Tikitin Muslim Muslim a 2023
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce goyon bayansa ga tikitin Muslim Muslim na 2023 ba na addini ba ne, dabarar siyasa ce kawai
- Ya bayyana cewa manufar tikitin ita ce lashe zabe, ba wai nuna wariyar addini ba, tare da bada misali da kwarewarsa a Kaduna
- El-Rufai ya ce babu Kirista da aka tauye wa hakki a Kaduna ko a Najeriya saboda wannan tikiti, domin shugabanci yana buƙatar kowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi magana kan goyon bayansa ga tikitin Muslim Muslim na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023.
Legit Hausa ta gano cewa Nasir El-Rufa'i ya yi magana ne bayan an tambaye shi tasirin hakan a siyasar Najeriya.

Source: Twitter
El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin shirin Channels Television, inda ya ce tsarin tikitin ba ya nuna wariya ga addini ko wata kabila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Muslim Muslim dabarar siyasa ce,' El-Rufa'i
A yayin tattaunawar, El-Rufai ya jaddada cewa tikitin Muslim Muslim na APC wata dabarar siyasa ce da aka tsara domin tabbatar da nasara a zaben 2023.
Ya ce:
“Dabarar siyasa ce; manufarta ita ce a ci zabe. Ba ta da alaka da addini. A lokacin da ake fafatawa, duk wata hanya da ka ga za ta baka nasara, kana amfani da ita.”
El-Rufai ya kara da cewa irin wannan tunani ya taimaka masa a Kaduna, inda ya taba yin tikitin Muslim Muslim ba tare da wani addini ya samu tawaya ba.
Maganar Muslim Muslim a zaben Kaduna
Tsohon gwamnan ya bada misali da irin kwarewar da ya samu a Kaduna. A cewarsa, a lokacin da ya zabi mataimakiya Musulma, babu wani Kirista da aka tauye wa hakki ko aka hana wakilci.
Ya ce:
“Na yi tikitin Muslim Muslim a Kaduna. Ina so a nuna min Kirista daya da aka tauye saboda wannan tsari. Shugaba da ke son nasara dole ya zabi mutane daga bangarori daban-daban.”
Ya kara da cewa, ba shugaban da ya ke so ya samu nasara da zai takaita ga addini daya ko kabila a lokacin da ya ke mulki.
Tarihin tikitin Muslim Muslim a 2023
Tikitin Muslim Muslim na APC ya kunshi Bola Ahmed Tinubu daga Kudu maso Yamma da Kashim Shettima daga Arewa maso Gabas, dukkansu Musulmai.
Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce a lokacin yakin neman zabe, inda wasu ke ganin zai haifar da wariya ga Kiristoci.
Sai dai a zaben shugaban kasa na watan Fabrairu 2023, Bola Tinubu ya lashe kujerar da kuri’u miliyan 8.79.

Source: Twitter
El-Rufai ya ce yanzu an kawar da duk wani tsoro da ake yi game da tikitin Muslim Muslim, domin ya tabbata cewa tsarin ba ya tauye hakkin kowa.
Malamai sun karyata ikirarin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa malaman addinin Musulunci da Kirista sun karyata wani ikirari da shugaba Bola Tinubu ya yi a Brazil.
A wani taro a kasar Brazil, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ikirarin cewa an riga an magance matsalar rashawa a Najeriya.
Sai dai a wani martani da malaman addini suka yi, sun ce ko kusa da magance matsalar ba a yi ba a Najeriya, wasu sun ce ba a dauki hanya ba ma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


