Muslim Muslim: Kungiyar APC Ta Yi wa Babachir Lawal Kaca Kaca kan Taɓa Shettima
- Kungiyar matasan APC, reshen Arewa maso Gabas (APC-YPNE) ta caccaki Babachir Lawal saboda kalamansa kan Kashim Shettima
- Shugaban kungiyar, Kabiru Garba Kobi ya zargi Babachir da raina Shettima tare da nuna kiyayyarsa a fili kan tikitin Muslima Muslmi na 2023
- A zantawarsa da Legit Hausa, Kobi ya ce hassada ce kawai ke cin Babachir, kuma yana ji yana gani Shettima zai kara daukaka a gwamnatin APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Kungiyar APC Youth Perliament, reshen Arewa maso Gabas ta yi kaca kaca da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.
Kungiyar matasan ta ce kalaman da Babachir Lawal ya furta kan mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima sun yi muni, kuma abin a yi wa Allah wadai.

Source: UGC
Shugaban APC-YPNE, Kabiru Garba Kobi, daga Bauchi, ya yi wannan sukar a zantawarsa da Legit Hausa a ranar Lahadi, 31 ga watan Agusta 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima: APC ta yi martani ga kalaman Babachir
Kabiru Garba ya ce kiran Kashim Shettima da 'dan amshin shata' da Babachir Lawal ya yi rashin girmamawa ce, kuma kiyayya karara ga lamba biyu a kasar.
Kungiyar matasan APCn ta kuma zargi tsohon sakataren gwamantin da raina mataimakin shugaban kasa da kuma yunkurin kawo tasgaro a gwamnatin Bola Tinubu.
APC-YPNE ta ce kiran Shettima ya yi murabus daga kujerarsa, ya nuna a fili, yadda Babachir Lawal yake adawa da tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi a 2023.
Kabiru Garba Kobi ya ce tun a 2023 Babachir Lawal yake fushi don an ba Shettima abokin takarar Tinubu, kuma shi ne har yanzu bai huce ba, yake sake fito da 'kiyayyarsa a fili.'
Me Babachir Lawal ya ce kan Shettima?
A baya bayan nan ne Babachir Lawal ya yi magana kan yadda Kashim Shettima ke gudanar da harkokin gwamnati matsayin mataimakin shugaban kasa.
Jaridar The Source ta rahoto Babachir ya kira Kashim Shettima da 'dan amshin shata,' abin da ke nufin babu wani abin azo a gani da mataimakin shugaban kasar yake yi a gwamnati.
Ya ce Kashim Shettima ya zama dan zuwa halartar bukukuwa, ko kananun tarurruka, ba tare da samun wani karfin iko a gwamnatin ta APC ba.
"Idan da ni ne shi, da na yi murabus daga mukamina, a mutunce," a cewar Babachir Lawal.
"Hassada yake yi wa Shettima' - Kabiru Kobi
Amma da yake mayar da martani kan kalaman tsohon sakataren gwamnati, shugaban kungiyar matasan APC, Kabiru Kobi, ya ce:
"Dole wannan magana ba za ta yi mana dadi ba. Ba zai yiwu mutumin da ya yi kwamishina, ya zama sanata, ya zama gwamna, aka kuma duba kwarewarsa aka ba shi mataimakin shugaban kasa, amma saboda wutar ciki, da mugunta, da kiyayya, da suka fito karara, da shi da tsohon kakakin majalisa, suka gwadawa duniya ba sa kaunar tikitin Muslim Muslim.
"Abin yana damunmu, a ce Babachir Lawal yana nuna kiyayya ga Musulunci da wasu masu mutunci a Arewa, abin ba ya mana dadi."
Kabiru Garba Kobi ya ce idan har Babachir yana ganin yana da kima, to ya tsaya takarar kujerar sanata a garinsa, yana mai cewa, "ai ta fi karfinsa ne, ba shi da aiki sai haddasa fitina, da bi-ta-da-kulli."
"Ba za mu yarda a taru a yi mana kudin goro a Arewa ba, a ce wasu daga cikinmu sun dage sai sun kawo mana wasi wasi, wajen tursasa mana wutar gabar kiyayyar siyasa ta addini."
- Kabiru Garba Kobi.
'Ba abin da Babachir ya yi wa Arewa' - Kobi

Source: UGC
Kungiyar matasan APC ta ce Babachir Lawal yana magana ne ba don yana kishin Arewa ba, sai don cika wani muradinsa na siyasa.
Shugaban kungiyar, Kabiru Kobi, ya ce:
"Wa ya taba taimaka wa a Arewa, ka gaya mun wata gidauniyarsa guda daya, ko gidan marayu da ya gina, ko maasana'anta guda daya, wacce shi Babachir Lawal ya gina don taimako, ko farfado da Arewa."
Kabiru Kobi ya ce Babachir yana fushi ne kawai saboda Tinubu bai dauke shi matsayin abokin takara a 2023 ba, kamar yadda ministan Abuja, Nyesom Wike ya fada a zantawarsa da Channels TV.
"Ya kamata dai mu 'yan Arewa mu so junanmu, mu rungumi gaskiya, mu fita sha'anin 'yan soki burutsu, masu son sai sun haddasa fitinar siyasa ta addini ko ta kabilanci a tsakaninmu."
- Kabiru Garba Kobi.
Wike ya yi wa Babachir saukale
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Nyesom Wike, ya ce har yanzu Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnati, yana cike da haushin Shugaba Bola Tinubu tun a 2023.
Ministan babban birnin tarayyar ya bayyana cewa kiyayyar Babachir ta samo asali ne bayan Kashim Shettima ya yi nasarar zamam abokin takarar Tinubu.
Wike ya ce Babachir Lawal ya sa ran cewa shi ne Tinubu zai zaba matsayin abokin takara, amma sai ya dauko Shettima daga Arewa maso Gabashin kasar.
Asali: Legit.ng



