El Rufa'i Ya Zargi Uba Sani da Tura Ƴan Daba don Tarwatsa Taronsu a Kaduna

El Rufa'i Ya Zargi Uba Sani da Tura Ƴan Daba don Tarwatsa Taronsu a Kaduna

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani ce ta shirya kai hari a taron adawa ƴan adawa
  • Furucin tsohon gwamnan ya biyo bayan wani hari da ƴan daba su ka kai wa taron haɗin gwiwa na jam'iyyun adawa a jihar a ranar Asabar
  • Da ya ke mayar da magana a fusace, Nasir El-Rufa'i ya sha alwashin kawo ƙarshen gwamnatin APC a Kaduna

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i ya bayyana mamaki a kan yadda aka kai wa taronsu hari a jihar.

A ranar Asabar, 30 ga watan Agusta, 2025 ne wasu ƴan daba suka kai hari inda aka tarwatsa taron jam’iyyun adawa a jihar, lamarin da ya haddasa fargaba.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro El Rufai a ADC, jiga jigan jam'iyya sun taso shi a gaba

An kai wa taron su El-Rufa'i hari
H-D: Hoton gwamna Kaduna mai ci, Uba Sani, tsohon ubangidansa, Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

A wani bidiyo da Arewa Updates ta wallafa a Facebook, El-Rufa’i ya zargi Gwamna Uba Sani da hannu a harin.

Wasu daga cikin hotuna da bidiyo bayan harin sun nuna yadda jama'a da dama suka jikkata yayin da aka ga wasu motoci da duwatsu ya huda gilasansu.

El-Rufa'i ya caccaki Uba Sani

A cewarsa, gwamnatinsa ba ta taɓa hana kowanne taro a Kaduna ba, ballantana ta take hakkin jama’a a baya.

El-Rufa’i ya ce:

"Ba mu taɓa kiran otal mun ce kada ku bari a yi taro ba. Wasu jihohi ma in ana son a yi taro, aka kasa, Kaduna ake zuwa a yi, domin mu ba ma yadda a taɓa hakkin kowa."
El-Rufa'i ya fusata
Hoton gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto:ImranMuhdz
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa:

"Amma abin takaicin shi ne, yaro na Uba Sani, wanda kullum yana bi na gurun-gurun kamar ya fahimci wadannan aƙidoji na kare hakkin al'umma da kuma kawo ci gaba da al'umma, shi ne ya ke jagorantar irin wannan."

Kara karanta wannan

'Yan daba sun tarwatsa taron ƴan adawa da El Rufa'i ya halarta a Kaduna, an ji raunuka

El-Rufa'i ya sha alwashin kan gwamnatin Kaduna

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya bar ƴan adawa da dama cikin rauni tare da bayan an lalata motocin da suka iso wajen taron.

El-Rufa’i ya bayyana takaici da zargin cewa Gwamna Uba Sani na da hannu a cikin lamarin, yana mai nuna cewa hakan ya saba koyarwarsa lokacin yana mulki.

Tsohon gwamnan ya yi alƙawarin cewa za a kawo ƙarshen gwamnatin APC a jihar Kaduna a zabe mai zuwa.

A cewarsa:

"Za a yi zabe, za a birne su."

Ƴan daba sun tarwatsa taron su El-Rufa'i

A baya, mun wallafa cewa a ranar Asabar, 30 ga watan Agusta, 2025, jam’iyyun adawa a jihar Kaduna su ka gudanar da gagarumin taron haɗin gwiwa a tsakanin ƴan adawa.

Jam'iyyun da su ka halarci taron sun haɗa da PDP, SDP, NNPP, LP, ADC, da wasu daga cikin APC da ke adawa da shugabancin jam'iyyar da gwamna Uba Sani a Kaduna.

Sai dai, wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun shigo wajen taron da makamai, daga ciki har da adduna, sanduna, da duwatsu, sannan su ka bi jama'a da suka har aka jikkata jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng