2027: APC Ta Cika Baki kan Yiwuwar Takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu
- Ana ci gaba da maganganu kan yiwuwar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake jaraba sa'arsa a zabe mai zuwa 2027
- APC reshen jihar Legas ta tsoma baki kan batun yiwuwar yin takara tsakanin tsohon shugaban kasan da Shugaba Bola Tinubu
- Jam'iyyar APC ta nuna cewa tsohon shugaban kasan ya shiga rudu kan abin da ya kamata ya yi a siyasance bayan doke shi a 2015
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi magana kan yiwuwar yin takarar tsakanin Goodluck Jonathan da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa tana bibiyar yadda ake ta rade-radin yiwuwar Goodluck Jonathan zai sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na gaba.

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Seye Oladejo, ya fitar a ranar Jumma'a, 29 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce akwai shakku kan tasirin tsohon shugaban kasan wajen iya kayar da Shugaba Bola Tinubu.
Akwai masu kiran Jonathan ya fito takara
Jonathan, wanda ya sha kaye a kokarin neman wa’adin mulki na biyu a zaben 2015, a hannun marigayi Muhammadu Buhari, na shan matsin lamba daga magoya bayansa kan ya sake neman kujerar a babban zabe na 2027.
Sai dai har yanzu tsohon shugaban kasan bai fito ya bayyana matsayarsa kan fitowa takara a zaben 2027 ba.
Me APC ta ce kan Goodluck Jonathan?
Kakakin na APC ya bayyana yanzu an wuce lokacin yin siyasar son kai, rahotom jaridar Tribune ya tabbatar.
"Duk da cewa mun amince da rawar da tsohon shugaban ya taka wajen tabbatar da mika mulki cikin lumana a shekarar 2015, wanda ya sa aka yaba masa a gida da waje."
"Dole ne mu bayyana a fili cewa Najeriya ta wuce siyasar son kai ko tunawa da baya."

Kara karanta wannan
"Tinubu ba zai iya ba," Babban Malami ya fadi wanda ya dace da mulkin Najeriya a 2027
"Kalubalen da muke fuskanta a yau da na gaba na bukatar shugabanci mai jarumta, kwazo da hangen nesa, ba wai komawa ga wani tsohon tsarin da ba ya cike da nasara ba."
"Yana da kyau a sani cewa ‘neman sa'a' kaɗai ba dabarar mulki ba ce."
- Seye Oladejo

Source: Facebook
Jam'iyyar APC ta caccaki Goodluck Jonathan
Seye Oladejo ya zargi gwamnatin Jonathan daga 2010 zuwa 2015 da barin kasar nan cikin rauni wanda ya hada da cin hanci da rashawa, tabarbarewar tsaro da kuma durkushewar tattalin arziki.
Bugu da kari, ya ce siyasar tsohon shugaban kasan ta shiga rudu sakamakon hulɗarsa da jam’iyyun siyasa daban-daban.
"Hulɗarsa da APC da kuma rashin tasirinsa a kokarin farfado da PDP, ya sa ayar tambaya kan amincinsa, hangen nesansa da kuma ainihin manufarsa ta siyasa."
- Seye Oladejo
Kungiyar SSRG ta ba Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar South-South Reawakening Group (SSRG), ta yi kira da babbar murya ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Kungiyar ta bukaci Jonathan da ya yi taka tsan-tsan kan masu kiransa da ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Ta bayyana cewa da yawa daga cikin masu neman ya fito takara, mutane ne wadanda suka kasance makiyansa lokacin da yake kan kujerar shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
