'Na Yi Kuskure a baya': Tsohon Sanata Ya Yi Azumi 31 domin Neman Jam'iyyar da Ta Dace
- Tsohon Sanata, Elisha Abbo daga jihar Adamawa ya bayyana kuskuren da ya tafka yayin sauya sheka a baya
- Sanata Abbo ya ce sai da ya yi azumi da addu’a har kwanaki 31 don neman dacewa kan siyasarsa bayan yin kuskure a baya
- Abbo ya tuna cewa a 2020 ya bar PDP zuwa APC ba tare da neman zabi wurin Allah ba, yana cewa ya yi nadama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Tsohon sanata daga Adamawa ta Arewa, Elisha Abbo, ya bayyana nadamar da ya yi a siyasarsa.
Sanata Abbo ya bayyana irin kuskuren da ya tafka yayin sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Source: Facebook
A cikin rubutu da ya wallafa a X ranar Juma’a 29 ga watan Agustan 2025, Abbo ya ce ya bar PDP zuwa APC a 2020 ba tare da addu’a ba.
Yadda Sanata Abbo ya bar PDP zuwa APC
An fara zaɓar Abbo sanata a 2019 a PDP kafin ya koma APC shekara daya bayan haka, amma kotu ta tsige shi a 2023 bayan ya zarce.
An shigar da Abbo kara a kotu game da zaɓen da aka gudanar wanda ake zargin almundahana da Sanata Yohanna ke kalubalantar zaɓen 2023.
Kotun daukaka kara ta bayyana Amos Yohanna na PDP a matsayin wanda ya lashe kujerar sanata na Adamawa ta Arewa, inda ta kori Abbo daga ofis.
Siyasa: Sanata Abbo ya koma ga Allah
Abbo ya bayyana cewa ya yi azumi da addu’a har na tsawon na kwanaki 31 don neman zabin Allah a siyasarsa.
Ya ce:
"A shekarar 2020 na bar PDP zuwa jam'iyyar APC ba tare da addu'a na neman zabin Allah ba domin neman jam'iyyar da zan shiga."

Source: Twitter
Kuskuren da Sanata Abbo ya yi a siyasa

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta
Tsohon sanatan ya ce a wancan lokacin ya bi son ransa kawai, ba tare da tuna Allah ba, ya shiga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya don bin yanayin siyasa kawai.
Abbo ya ce yanzu yana neman shiriya daga Allah kafin barin APC, domin ya fahimci muhimmancin addu’a a irin wannan babban mataki.
Ya kara da cewa:
"Wannan karo, na yi addu'o'i da azumi har na tsawon kwanaki 31 domin neman zabin Allah da sauran abubuwan da nake son Ubangiji ya cika mani.
"Nan ba da jimawa ba, zan fitar da sanarwa a hukumance bayan tuntuba ta karshe kan lamarin."
Abbo ya ce yanzu ba ya yin siyasa da son kai, sai dai bisa jagorancin Ubangiji da tattaunawa cikin natsuwa.
Natasha: Sanata Abbo ya caccaki Akpabio
A baya, mun ba ku labarin cewa tsohon Sanata daga jihar Adamawa, Elisha Ishaku Abbo ya zargi Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da nuna son rai.
Haka kuma ya zarge shi da amfani da karfin iko wajen dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga majalisar dattawa.
Tsohon Sanatan ya bayyana takaicin yadda majalisar kasar nan ta raina hukuncin kotu, tare da karfa-karfa wajen gudanar da aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
