Yanzu-yanzu: Sanata Ishaku Abbo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Sanata Ishaku Abbo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Jam'iyyar PDP ta sake babban rashi a majalisar dokokin tarayya

- Wannan ya biyo bayan sauya shekara gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi

- Uwar jam'iyyar ta ce ba zata yar da wannan abu ba, za ta je kotu

Sanata mai wakiltan Adamawa ta Arewa, Elisha Ishaku Abbo, ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, zuwa masu rinjaye All Progressives Congress, APC.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana sauya shekan Abbo a wasikar da ya karanta ranar Laraba a zauren majalisa.

A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP be saboda salon mulkin gwamnan jihar Adamawa, Umaru Ahmed Fintiri.

Sauya shekar Ishaku Abbo ya biyo bayan fita daga jam'iyyar da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi yayi makon da ya gabata.

Da alamun akwai baraka cikin 'yayan jam'iyyar PDP yayinda aka fara maganganun zaben 2023.

KU KARANTA: Baka isa ka tafi da kujeranmu ba - Uwar jam'iyyar PDP ta gargadi Sanatan da ya sauya sheka APC

Yanzu-yanzu: Sanata Ishaku Abbo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Yanzu-yanzu: Sanata Ishaku Abbo ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Asali: Original

Hakan ya sa jam'iyyar ta kafa kwamiti na musamman domin sulhu tsakanin 'yayayn jam'iyyar a fadin tarayya.

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta nada tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a matsayin shugaban kwamitin sulhu na kasa mai mambobi guda shida.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Pius Ayim; tsaffin gwamnoni Liyel Imoke (Cross Rivers), Ibrahim Dankwambo (Gombe) da Ibrahim Shema (Katsina) da kuma tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Mulikat Akande.

KU KARANTA: An damke mahaifiya tana kokarin sayar da jaririnta kudi N150,000

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel