Gwamna Ya Jero Mutum 2 da PDP ke Tunanin Tsaida wa Takarar Shugaban Kasa a 2027
- A farkon wannan makon ne jam'iyyar PDP ta yanke shawarar bai wa Kudu takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa
- Babbar jam'iyyar adawa ta dauki wannan matsaya ne a taron kwamitinta na zartarwa (NEC) wanda ya gudana ranar Litinin da ta shude
- Shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce tuni suka fara nazari kan wanda za su ba takara a Kudu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa PDP ta fara laluben wanda ya kamata ta tsaida takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Gwamnan ya ce bayan yanke shawarar yankin da za a dauko dan takara, PDP ta fara nazari kan yiwuwar tsaida daya daga cikin manyan yan siyasa biyu daga Kudu.

Source: Twitter
Sanata Bala ya bayyana haka ne a cikin shirin Politics Today na tashar Channels tv ranar Alhamis, 28 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum 2 da PDP ke tunanin ba takara
Gwamna Bala ya ce mutum biyu da PDP ke nazarin tsaida daya daga ciki takara su ne tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da dan takarar LP a 2023, Peter Obi.
Bala Mohammed ya ce Jonathan, wanda ya bayyana a matsayin “ɗan siyasa mafi farin jini a yau”, ya yi fama da kazafin siyasa kafin zaben 2015, amma daga bisani kotu ta wanke shi.
Tsohon ministan Abuja ya kuma bayyana cewa Obi, wanda ya tsaya takara a 2023 karkashin jam’iyyar LP, zai samu dama idan ya koma PDP, rahoton Tribune Nigeria.
“Tabbas, tsohon shugaban ƙasa Jonathan yana daga cikin mutanen da muke tunani a kana'su idan ya yarda zai fito takara.
"Har da mutane irin su tsohon gwamna Obi, domin idan ya yanke shawarar dawowa dandalin siyasa mafi karfi (PDP), zai samu dama,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya hango hadarin da PDP za ta shiga idan ta tsayar da Jonathan takara a 2027
Shin PDP tana kokarin dawo da Peter Obi?
Da aka tambaye shi ko gwamnonin PDP na tattaunawa da Obi kan yiwuwar tsayawa takara a karkashin jam’iyyar, sai ya ce:
“Ba ku gan shi tare da ni ba? Ɗan uwana ne, abokina ne. Kuma shi ma yana daga cikin fitattun ‘yan siyasa. Duk da ya shiga hadaka, muna ci gaba da aiki a hankali ba tare da hayaniya ba.”

Source: UGC
Gwamna Bala, wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP, ya ƙara da cewa akwai sauran ‘yan jam’iyyar daga Kudu irin su gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da suke da ‘yancin tsayawa takara.
“Akwai ‘yan siyasa da yawa. Na yi zama ma da tsohon gwamna Amaechi. Ba na barci, ina ƙoƙari na haɗa kan mutane domin su zo su taimaka,” in ji shi.
Wani dan PDP a jihar Katsina, Rabiu Yusuf ya bayyana cewa jawo Jonathan ko Obi ba shi ne mafita ba, ya zama dole a warware matsalolin cikin gida.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, jigon ya ce kowa PDP ta tsayar takara matukar ba ta magance matsalar cin amanarta da ake yi ba, to ba za ta canza zani ba.
"Jonathan mutum ne da ke da farin jini da karbuwa a Kudu da Arewa, Peter Obi yana da karfi a siyasa, amma fa duk ba su ne asalin matsalar PDP ba.
"Kowa muka tsaida matukar gwamna zai iya fitowa ya ce zai marawa wani dan jam'iyya daban baya, to akwai matsala, mu fara toshe barakar gida kafin mu fita waje," in ji shi.
Gwamna ya nemi PDP ta kaucewa kuskuren APC
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Bauchi ya bayyana cewa PDP na bukatar dauko dan takarar daga Kudu kuma kirista domin fafatawa da Tinubu a zaben 2023.
Gwamna Bala ya ce hakan ne zai sa PDP ta guji aikata kuskuren da jam’iyyar APC ta yi a 2023, lokacin da ta fito da tikitin Musulmi da Musulmi.
A cewarsa, har yanzu Najeriya ba ta kai matakin da za ta yi watsi da addini da yanki wajen raba manyan mukamai ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

