'Mun Dauki Darasi,' Gwamna Ya Fadi Babban abin da Ya Jawo PDP Ta Fadi Zaben 2023
- Gwamna Bala Mohammed ya ce kuskuren da PDP ta yi na ba dan Arewa, tikitin takara a 2023 ya jawo faduwar jam'iyyar a zabe
- Gwamnan jihar na Bauchi, ya yi nuni da cewa, PDP na da damar da za ta iya lashe zaben na baya da ace ta ba dan Kudu tikiti
- Yanzu da PDP ta koyi darasi, Gwamna Bala ya ce jam'iyyar ta mika tikiti ga Kudu, kuma zai so a ce kirista aka tsayar takara a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa jam’iyyar PDP ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewar Gwamna Bala Mohammed, kin baiwa yankin Kudu tikitin shugaban kasa da PDP ta yi ne ya jawo ta sha kasa a hannun APC.

Source: Twitter
"PDP ta koyi darasi" - Gwamna Bala
Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya bayyana haka ne a shirin 'siyasa a yau' na Channels TV a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabinsa na zuwa ne kwanaki kadan bayan jam’iyyar ta mika takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya a zaben 2027.
Gwamnan ya ce:
“Rayuwa, tana zama darasi a koyaushe. Rashin ba Kudu tikiti a 2023 ya sa muka sha kaye. Na kuma gane cewa shugabanci lamari ne na amincewar kowa, ba wai mutum zai tilasta wa wasu ra’ayinsa ba.”
Rikicin PDP da tasirin gwamnonin G-5
A lokacin shirye-shiryen zaben 2023, PDP ta bude tikitin takara ga kowa, abin da ya ba tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar damar yin takara.
Wannan matakin ya tayar da kura a cikin PDP, inda gwamnonin G-5 karkashin tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, suka nuna adawa.
Wike, wanda ya sha kaye a zaben fitar da gwani ga Atiku, ya bayyana cewa rashin daidaito wajen rarraba tikitin PDP, shi ne babban rashin adalci ga Kudu.
Ya yi nuni da cewa tun da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Arewa ya kammala shekaru takwas a mulki, kamata ya yi mulki ya koma Kudu.
Saboda wannan rikicin, Wike ya yi watsi da PDP tare da goyon bayan Tinubu, wanda daga bisani ya nada shi ministan babban birnin tarayya.

Source: Twitter
2027: PDP ta mika tikiti zuwa Kudu
Domin guje wa maimaita irin wannan rikici, PDP ta yanke shawarar tsayar da ɗan takararta daga Kudu a zaben 2027.
Shugabannin jam’iyyar adawar, karkashin Ambasada Umar Damagum, sun bayyana cewa hakan zai tabbatar da adalci da gyara kura-kuren baya.
Gwamna Bala Mohammed ya ce:
“Lokacin da jam’iyyata ta yanke shawarar rarraba tikitin zuwa Kudu, ban ga wata matsala ba, saboda na san yin hakan alheri ne, babu son rai a ciki. Mun koyi darasi daga abin da ya faru a baya.”
'PDP na bukatar kirista daga Kudu' - Gwamna
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP tana bukatar ɗan takara kirista daga Kudu wanda zai kara da Shugaba Bola Tinubu a 2027.
A cewar gwamnan na Bauchi, gwamnatin APC ta tafka kuskure a 2023 na yin takarar Musulmi da Musulmi, kuskuren da ya ce PDP ba za ta yi ba a 2027.
Gwamna Bala Mohammed ya ce tsayar da dan takara Kirista daga Kudu da mataimaki Musulmi daga Arewa ne zai kawo daidaito a jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng


