"PDP na Buƙatar Ɗan Takara Kirista daga Kudu,' Gwamna Bala Ya Yi Magana kan 2027

"PDP na Buƙatar Ɗan Takara Kirista daga Kudu,' Gwamna Bala Ya Yi Magana kan 2027

  • Da alama, babbar jam'iyyar adawa ta PDP za ta tsayar da Kirista a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben 2027
  • Gwamna Bala Mohammed ya ce tsayar da dan takara Kirista daga Kudu da mataimaki Musulmi daga Arewa ne zai kawo daidaito
  • Amma ba iya daidaito kawai ba, gwamnan Bauchi ya ce wannan tsarin ne zai sa PDP ta guji maimaita kuskuren da APC ta yi a 2023

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa akwai bukatar jam’iyyar PDP ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu, kuma Kirista a 2027.

Gwamna Bala ya ce hakan ne zai sa PDP ta guji aikata kuskuren da jam’iyyar APC ta yi a 2023, lokacin da ta fito da tikitin Musulmi da Musulmi.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa PDP ke son ɗan takarar shugaban ƙasa Kirista saɓanin APC'

Gwamnan Bauchi ya kawo shawarar PDP ta tsayar da dan takara Kirista daga Kudu a zaben 2027
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed yana jawabi a Bauchi, da shugaban PDP, Umar Damagum a ofishin jam'iyyar a Abuja. Hoto: @SenBalaMohammed, @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Gwamnan jihar Bauchin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Siyasa a yau' a gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: PDP za ta guji kuskuren APC

Yayin da ya ce kofar jam’iyyar PDP a buɗe take ga duk masu sha'awar tsaya wa takara, ya kuma ce dole ne a yi hankali wajen zaɓen ɗan takarar.

“Ba mu goyi bayan wani yanzu ba, amma na yi imani cewa lokaci ya yi da za mu fito da Kirista daga Kudu, wanda zai samu mataimakin shugaban kasa Musulmi daga Arewa.
"Wannan zai tabbatar da daidaito da kuma mutunta bambancinmu. Ba ma so mu maimaita kuskuren APC, lokacin da suka fito da Musulmi daga Kudu da kuma Musulmi daga Arewa, wanda ya saba da ra’ayoyin al’umma.'

- Gwamna Bala Mohammed.

Gwamnan ya ƙara da cewa har yanzu Najeriya ba ta matakin da za ta yi watsi da addini da yanki wajen raba manyan mukamai ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya rufe bakin masu yada jita jitar zai koma jam'iyyar APC kafin zaben 2027

A cewarsa, takarar Muslim Muslim da jam'iyyar APC ta yi a 2023 ya kawo ce-ce-ku-ce da rashin jituwa a tsakanin ’yan ƙasar.

Gwamna ya musanta zancen tikitin Makinde-Mohammed

Gwamnan Bauchi ya kuma musanta rade-radin da ke cewa PDP na shirin tsayar da Seyi Makinde, gwamnan jihar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da shi a matsayin mataimaki.

Kauran Bauchi ya ce:

“Ba haka muke shirin yi ba. Na yi aiki tare da shugaban ƙasa lokacin ina ministan Abuja, kuma na fahimci cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ne ke da ikon zaɓar mataimakinsa.
"Ni ba zan tsaya ina jiran kujerar mataimakin shugaban ƙasa ba. Amma idan shugabannin jam’iyya da ɗan takara suka yanke shawarar zaɓa ta, zan amince. Idan kuma ba ni suka zaɓa ba, zan goyi bayan wanda ya dace daga Kudu.”
Gwamna Bala Mohammed ya ce ba gaskiya ba ne rade-radin da ake yadawa cewa zai yi wa Makinde mataimaki a 2027.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, yana jawabi a wani taro a birnin Ibadan. Hoto: @seyiamakinde
Source: Facebook

Tikitin Musulmi da Musulmi a 2023

A baya, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya zaɓi tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima, a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.

Wannan matakin ya jawo suka daga ’yan Najeriya da dama, musamman saboda kasancewar su biyun Musulmai ne daga Arewa da Kudu.

Kara karanta wannan

Tinubu: Bayan an yi mata ca, PDP ta faɗi dalilin tura takarar shugaban ƙasa ga Kudu

Jam’iyyar PDP dai ta riga ta bayyana cewa ta mika tikitin shugaban ƙasarta zuwa Kudancin Najeriya a 2027, abin da ke nufin jam’iyyar za ta tsayar da ɗan takararta daga yankin.

Gwamna Bala ya jingine burin takara

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi karin haske kan jingine burninsa na yin takarar shugaban kasa.

Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa burinsa na zama shugaban kasa bai kai girman hadin kan Najeriya ba, don haka zai goyi bayan wanda PDP ta tsayar.

Gwamnan ya kuma nuna cewa yana goyon bayan matakin jam'iyyar adawa ta PDP na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com