"Tinubu ba Zai Iya ba," Babban Malami Ya Fadi Wanda Ya Dace da Mulkin Najeriya a 2027

"Tinubu ba Zai Iya ba," Babban Malami Ya Fadi Wanda Ya Dace da Mulkin Najeriya a 2027

  • An yi hasashen cewa da yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha kasa a kokarinsa na neman tazarce a zaben 2027
  • Wani babban fasto da ya shahara wajen hasashen abin da zai faru, Adeyeye da ke birnin Ibadan ya ce Jonathan zai iya komawa kan mulki
  • Malamin addinin ya ce tsohon shugaban kasar na da damar sake darewa kujerar shugabancin Najeriya idan har ya tsaya takara a 2027

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Wani malamin addinin Kirista daga Ibadan, Apostle Oluwarotimi Adeyeye, ya yi hasashen sakamakon zaben shugaban kasa na 2027.

Fitaccen faston, shugaba kuma wanda ya kafa cocin Clear Revelation Ministry, ya hango faduwar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.
Hoton tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan a wurin taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Fasto ya hango nasarar Jonathan a 2027

A rahoton Tribune, faston ya yi hasashen cewa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan zai lashe zaɓen shugaban ƙasar 2027 idan ya yanke shawarar tsayawa takara.

Kara karanta wannan

2027: Amaechi ya sha sabon alwashi kan takarar shugaban kasa karkashin ADC

Fasto Adeyeye ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar kungiyar 'yan jarida (NUJ) ta reshen Ibadan, ranar Laraba, inda ya gabatar da hasashensa na shekara.

Malamin, wanda a baya ya taɓa yin hasashen tsigewa da kuma dawo da tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja, ya ce:

“Idan Jonathan ya yanke shawarar sake tsayawa takara a kowace jam’iyya da aka yi wa rijista, Allah zai iya dawo da shi kan karagar mulki.”

A cewarsa, tun a 2014 lokacin da ya hadu da Engr. Jide Adeniji a Barikin Dodan da ke Legas, ya fahimci cewa Jonathan yana da zuciyar yarda da nufin Allah.

'Abin da ya sa Allah zai iya dawo da Jonathan'

Ya ce hakan ya tabbata lokacin da Jonathan ya ƙi amincewa da tayin Amurka kan auren jinsi, da lokacin da ya amince ya bar ofis a 2015 domin tabbatar da zaman lafiya a Najeriya bayan ya sha kaye.

Kara karanta wannan

"Ya godewa Allah": Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ba Tinibu shawara kan 2027

“Da bai amince ya sauka daga mulki a wancan lokaci ba, da Najeriya ta fada cikin rikici da zubar da jini. A 2013 na yi taron manema labarai na duniya inda na ce Jonathan na iya zama shugaban kasa na ƙarshe a PDP.
"Amma yanzu, idan har Najeriya ta ci gaba da tsayuwa a matsayin ƙasa ɗaya, Allah na iya mayar da shi ofis sau ɗaya,” in ji shi.
Shugaba Tinubu da Jonathan.
Hoton Shugaba Bola Tinubu tare da Jonathan Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Malamin coci ya shawarci Tinubu ya hakura

Game da burin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin tazarce, malamin ya shawarci mai girma shugaban kasa da ya janye, rahoton Daily Post.

“Ban ga alamar zai samu nasara a zabe mai zuwa ba, amma a wurin Allah babu abin da ba zai yiwu ba,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga shugabannin ƙasar da su tuba daga halayensu marasa kyau domin Najeriya ta samu ci gaba.

An ci gaba da kokarin jawo Jonathan kafin 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Mathias Tsado ya bukaci makusantan Goodluck Jonathan da su lallashe shi ya hakura ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce dawowar Jonathan kan mulki ita ce mafita mafi dacewa wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke kara ta’azzara.

Ya ce mulkin Jonathan ya bar kyakkyawan tarihi wajen bin ka’idojin dimokuraɗiyya da sauye-sauye da za a iya farfaɗowa da su

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262