"Na Hakura": Gwamna Bala Ya Bayyana Dalilin Jingine Burin Yin Takarar Shugaban Kasa

"Na Hakura": Gwamna Bala Ya Bayyana Dalilin Jingine Burin Yin Takarar Shugaban Kasa

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi karin haske kan jingine burninsa na yin takarar shugaban kasa
  • Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa burinsa na zama shugaban kasa bai kai girman hadin kan Najeriya ba
  • Gwamnan ya nuna cewa yana goyon bayan matakin jam'iyyar PDP na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana dalilinsa na ajiye burin takarar shugaban kasa.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya ajiye burinsa na neman shugaban kasa a gefe, domin ci gaban jam’iyyar PDP da haɗin kan Najeriya gaba ɗaya.

Gwamnan Bala Mohammed ya ce ya hakura da takarar shugaban kasa
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, yana jawabi a wajen wani taro Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bayanin na sa ya biyo bayan matakin da PDP ta ɗauka a ranar Litinin, inda ta kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu, sannan ta bar kujerar shugaban jam’iyya a Arewa.

Kara karanta wannan

Ina makomar Tinubu?: APC ta ce za ta ba kowa dama ya tsaya takarar shugaban ƙasa

Meyasa Gwamna Bala ya hakura da takara?

Gwamna Bala Mohammed ya ce ya yanke shawarar janye burinsa na shugabancin kasa ne, domin girmama tsarin jam’iyya da kuma ba wasu damar samun adalci wajen cimma burinsu.

Ya ce tuni ya gamsu da irin hidimar da ya yi wa kasar nan a fannoni daban-daban, ciki har da kasancewarsa ministan babban birnin tarayya Abuja a baya, rahoton Channels tv ya tabbatar.

"Burina bai fi Najeriya girma ba, kuma tabbas bai fi jam’iyya girma ba. Idan ban zama shugaban kasa ba, na rike manyan mukamai a baya, kuma ina godiya da hakan."
"Na yi matukar gamsuwa da wannan matsaya. Na kasance cikin tattaunawa daga shirin tun farko har zuwa yanke hukuncin karshe. Tsari ne da ya haɗa kowa da kowa."

- Gwamna Bala Mohammed

Gwamna Bala na son hadin kai a PDP

Gwamna Bala ya ce muhimmin abu shi ne jam’iyyar ta amince da ci gaba da bin tsarin raba mukamai na yanzu, sannan ta bai wa Kudu damar tsayar da ɗan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Gwamna Bala ya kare matakin PDP na kai takara shugaban kasa zuwa Kudu
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Mohammad, yana jawabi a wajen taro Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Facebook

Ya ce wannan zai ƙara haɓaka haɗin kai, fahimta da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar.

"Ina so ’yan Najeriya su fahimci cewa siyasa ba wai don son rai ba ce. Siyasa batun cika buri ne a cikin tsarin jam’iyya, manufofin jam’iyya da ci gaban kasa."
"Duk wani abu dole ya ginu ne bisa sadaukarwa ba son kai ba. Ya kamata mu rayu tare da juna, mu girmama juna, mu gane cewa mulki daga Allah ne."

- Gwamna Bala Mohammed

Gwamna Bala ya ba dan China mukami

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dauko dan kasar China ya ba shi mukami a gwamnatinsa.

Gwamna Bala Mohammed ya nada Mr. Li Zhensheng a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki.

Bala Mohammed ya bayyana cewa matakin da ya dauka na nada Mr Li Zhensheng zai sanya jihar Bauchi ta shiga sahun gaba wajen kulla alaka da kasashen duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng