APC Ta Nakasa Dan Siyasar da Jam'iyyar PDP Ta ke da Shi a Kaduna
- 'Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a zaben 2023 a Jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan, ya samu tangarda a tafiyar siyasarsa a jihar
- Rahotanni sun tabbatar da cewa ya gaza shawo kan shugaban PDP na Kudan, Sanusi Magaji da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
- Alhaji Magaji, wanda aka fi sani da Mai Kwando, ya samu babban mukami da shugaban ƙaramar hukumar Kudan ya ba shi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Siyasar 'dan takarar gwamnan jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Alhaji Isa Ashiru, ta samu tasgaro.
Rahotanni na cewa ta kasa jawo tsohon shugaban mazabar Kudan, Hon. Sanusi Magaji, wanda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a baya-bayan nan.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Kudan shawara kan harkokin siyasa da hulɗa da jama’a, Alhaji Yunusa Chiroma, ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Dauda Iliya Abba, ya ƙarfafa siyasarsa bayan ya ba Sanusi Magaji gwaggwaban mukami.
'Dan takarar PDP ya samu matsala a Kaduna
Trust radio ta ruwaito cewa Hon. Abba ya naɗa Sanusi Magaji, wanda aka fi sani da Mai Kwando, a matsayin mai bashi shawara na musamman.
Zai mayar da hankali ne a kan ƙarfafa al’umma da tsare-tsaren a rumfunan zaɓe, matakin da ake ganin zai kara wa APC karfi a yankin.

Source: Twitter
Sanarwar ta bayyana cewa Sanusi Magaji ya bar jam’iyyar PDP ranar 11 ga watan Agusta 2024, inda aka yi ƙoƙarin shawo kansa ya fasa sauya sheƙa.
Haka kuma sanarwar ta ce an yi kokarin ko da zai sauya shekar, to ya koma jam’iyyar ADC ko SDP, amma ya ƙi amincewa da hakan.
A cewar sanarwar:
“Da wannan naɗi, Hon. Magaji ya zama ba kawai ɗan APC ba, amma ginshiƙi mai ƙarfi a jam’iyyar. Haka kuma Hon. Dauda Iliya Abba ya tabbatar da karfinsa a siyasar Kudan."
Dalili baiwa Mai Kwando mukami a APC
Alhaji Yunusa Chiroma ya bayyana cewa wannan matakin baiwa na hannun daman 'dan takarar PDP mukami ya biyo bayan yadda ya yi watsi da PDP.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“A cikin ƙasa da shekara guda, shugabannin PDP da sauran manyan jiga-jiganta sun fice daga jam’iyyar a Kudan suka koma APC. Wannan ya nuna cewa Isa Ashiru na rasa ƙimar sa a siyasarsa yankinsa, abin da ke sa mutane su fara kokwanto kan sake tsaya takara a matsayin gwamna a nan gaba.
Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa shigar Hon. Sanusi Magaji Mai Kwando cikin APC na nuni da yadda jam’iyyar mai mulki ke da niyyar ƙarfafa kanta a kananan hukumomi.
'Yan jam'iyyar PDP sun fusata a Kaduna
A wani labarin, mun wallafa cewa PDP reshen Kaduna ta bayyana damuwa kan tsare ’yar takararta na zaɓen cike gurbin kujerar Chikun/Kajuru a majalisar wakilai, Princess Esther Ashivelli Dawaki.
Shugaban PDP na jihar, Sir Edward Percy Masha, ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce lamarin na nuna yunƙurin hana 'yan adawa tasiri a jihar.
Ya ce EFCC ta gayyaci Princess Esther da daraktan yakin neman zabenta, Alhaji Shehu Fatangi kuma tun daga wannan lokaci tana tsare a hannun hukumar har yanzu babu labarin sakinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


