"Ya Godewa Allah": Tsohon Dan Shugaban Kasa Ya Ba Tinubu Shawara kan Zaben 2027

"Ya Godewa Allah": Tsohon Dan Shugaban Kasa Ya Ba Tinubu Shawara kan Zaben 2027

  • Ana ta maganganu kan batun tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaben shekarar 2027 duk da akwai lokaci
  • Wasu na ganin cewa Shugaba Tinubu ya cancanci ya yi tazarce, yayin da wasu ke ganin ya kamata 'yan Najeriya su raba shi da madafun ikon kasar nan
  • Adewole Adebayo na ganin cewa idan abubuwa ba su sauya zani ba, kyau shugaban kasar ya hakura ya koma gida a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, Adewole Adebayo, ya yi magana kan kamun ludayin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Adewole Adebayo ya bayyana cewa har zuwa yanzu Shugaba Bola Tinubu, bai yi abin da za a yaba masa ba, kuma ayyukansa ba su gamsar ba.

Adewole Adebayo ya ba Tinubu shawara
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Adewole Adebayo Hoto: @DOlusegun, @PrinceAdebayo
Source: Twitter

Adewole Adebayo ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 27 ga watan Agustan 2025, yayin da yake amsa tambayoyi a shirin Politics Today na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Bayan kwashe kwanaki a kasashen waje, jirgin Shugaba Tinubu ya iso Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Shugaba Tinubu?

Tsohon dan takarar shugaban kasan ya shawarci Shugaba Tinubu, da ya daina tunanin yin takara karo na biyu idan abubuwa ba su inganta kafin zaɓen gaba ba.

Hakazalika ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da rashin iya tafiyar da al’amuran kasar nan yadda ya kamata.

"Saboda haka ban yi imani cewa idan abubuwa suka ci gaba da kasancewa haka zuwa shekarar 2027 ba, Shugaba Tinubu, da zuciya ɗaya, zai yi mamaki idan aka kada shi a zaɓe ba."
"Yan Najeriya sun sha wahala ƙwarai. Manufofinsa ba sa aiki.”
"Na yi imani cewa dole ne mu fahimci cewa ’yan Najeriya suna da zabi. Amma idan zuwa 2027 abubuwa sun sauya, ta fuskar tattalin arziki, tsaro, talauci da samar da ayyukan yi, za a fafata a zaɓen."
"Amma yadda abubuwa suke yanzu, ina ganin abin da ya fi ga kasar, har ma da shi kansa shugaban kasa, ya kamata kawai ya koma gida ya gode wa Allah da ya ba shi damar shugabancin kasa na shekaru huɗu."

Kara karanta wannan

"An makara": Hadimin Wike ya hango kuskure kan matakin PDP na kai tikitin takara Kudu

- Adewole Adebayo

Adewole ya yi watsi da kai tikitin PDP Kudu

Maganarsa ta zo ne kwanaki kaɗan bayan babbar jam’iyyar adawa ta kasa watau PDP, ta ayyana cewa ta kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin kudu a shekarar 2027.

Sai dai jigon na SDP ya nuna cewa wannan mataki na PDP ba shi da wani muhimmanci sosai, domin ’yan Najeriya suna da zabi a zaɓen da ke tafe.

Adewole Adebayo ya ce APC da PDP duk abu guda ne
Tsohon dan takarar shugaban kasa na SDP a 2023, Adewole Adebayo, yayin da yake jawabi ga manema labarai Hoto: @PrinceAdebayo
Source: Twitter
"Baya ga PDP, muna da zabi sosai, don haka ba wai idan PDP ta lalata kanta, APC ce za ta gaji siyasar kasar nan ba. A’a.”
"Abin da muka sani shi ne APC da PDP kamar ’yan tagwaye ne, abu ɗaya ne yanzu. Suna aiki tare. ’Yan Najeriya suna son siyasa ta daban. Muna neman sabon shugabanci, sabuwar hanya. Wannan shi ne abin da jama’a ke faɗi.”

- Adewole Adebayo

'Yan majalisun PDP sun taso Tinubu a gaba

Kara karanta wannan

JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP sun ragargaji Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan rashin tsaro.

'Yan majalisar sun bayyana cewa 'yan Najeriya na mutuwa saboda matsalar tsadar rayuwa da halin kuncin da suka tsinci kansu a ciki.

Sun bukaci Shugaba Tinubu da ya katse yawace-yawacen da yake yi, ya dawo gida domin fuskantar matsalolin 'yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng