An Gudu An Dawo: Shugaban APC Ya Nemi Taimakon Ganduje, Ya Tona Maganarsa da Tinubu

An Gudu An Dawo: Shugaban APC Ya Nemi Taimakon Ganduje, Ya Tona Maganarsa da Tinubu

  • Shugaban jam’iyyar APC, Nentawe Yilwatda, ya roki tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje alfarma game da ayyukansa
  • Nentawe ya bayyana Ganduje a matsayin shugaban hadin gwiwa na jam'iyyar da ke mulkin Najeriya
  • Sabon shugaban APC ya ce zai dogara da kwarewarsa wajen karfafa jam’iyyar da ci gaba domin ba ta nasara a zabukan da ke tafe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana muhimmancin Abdullahi Umar Ganduje.

Farfesa Nentawe ya bayyana shirinsa na hada kai da Ganduje domin kawo ci gaba da hadin kai a jam'iyyar.

APC ta nemi taimakon Ganduje
Shugaban APC da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Facebook

Ganduje: Taimakon da sabon shugaban APC ke nema

Farfesa Yilwatda ya yi wannan jawabi ne a Abuja, lokacin da Ganduje ya kawo masa gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa da ta rasu kwanakin baya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Ina makomar Tinubu?: APC ta ce za ta ba kowa dama ya tsaya takarar shugaban ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yilwatda ya bayyana cewa zai dogara da gogewa, shawarwari, da dangantakar siyasa ta Ganduje domin karfafa APC tare da gina ingantacciyar jam’iyya mai karfi.

Shugaban APC ya ce ya dauki Ganduje a matsayin 'shugaban hadin gwiwa', inda ya bayyana cewa Tinubu ya umurce shi ya yi aiki tare da shi.

Yilwatda ya ce:

“Kofar ofishina a bude take, abokantaka a bude take, na fada wa shugaban kasa zan dauke ka a matsayin shugaba.
“Ina aiki domin hada kai. Aiki na shi ne hada mambobin jam’iyya. Amma jam’iyyar tamu ce gaba daya.”
Ganduje ya ziyarci sabon shugaban APC a Abuja
Sabon shugaban APC, Nentawe da Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Nentawe ta yaba da kwarewar Abdullahi Ganduje

Shugaban APC ya bayyana cewa gogewar Ganduje tun daga zamanin jam’iyyar NPN ta 1980s, ta sanya shi cikin mutane masu iya bayar da shawarwari masu muhimmanci.

Ya kara da cewa:

"A lokacin kai kana cikin harkar siyasa, mu kuma daliban firamare ne. Saboda haka, har yanzu muna bukatar shawarwarinka.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

Ya jaddada cewa zai dogara da dangantaka, gogewa, da kwarewar Ganduje domin gina jam’iyyar tare da tabbatar da nasarorin siyasa a gaba.

Ganduje ya yi jawabi mai jan hankali

A nasa jawabin, Ganduje ya ce dangantakarsa da sabon shugaban jam’iyya ya zama misali na kyakkyawar alaka tsakanin wanda ya sauka da wanda ya gaje shi.

Abdullahi Ganduje ya ce wasu tsofaffin gwamnoni suma suna da matsaloli da wadanda suka gaje kujerunsu a jihohi daban-daban, cewar The Guardian.

Ganduje ya ce:

“Tsofaffin gwamnoni da magadansu suna da matsaloli a Najeriya. Amma wannan dangantaka tana zama mafita ga jam’iyya da tsarin dimokuradiyya gaba daya.”

Ya kammala da taya Yilwatda murna bisa nadinsa, tare da jaddada cewa dangantakar su za ta zama abin koyi ga siyasar Najeriya baki daya.

Bayan dawowa daga London, Ganduje ya wuce ta'aziyya

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo daga London inda ya shafe kwanaki bayan saukarsa daga shugabanci.

Da isowarsa Najeriya, ya kai ziyara ta musamman ga Gwamna Usman Ododo na Kogi domin yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifinsa.

Haka kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa gidan Ododo domin jajanta musu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.