Bayan Tura Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Kudu, PDP Ta Magantu kan Jajubo Jonathan
- A kwanakin nan jam'iyyar PDP ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya domin zaben 2027
- Kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya yi magana kan haka da kuma matsayarsu game da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
- Ologunagba ya ce PDP yana da ƙwararrun ’yan takara, ya kuma ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa game da Peter Obi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Bayanai suna kara bullukowa kan alakar jam'iyyar PDP da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya yi magana kan alakar bayan tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu.

Source: Getty Images
Ologunagba ya fadi hakan ne yayin hira da tashar Arise News inda ya yi martani kan jita-jita game da takarar shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta tura tikitin shugaban kasa Kudu
Hakan na zuwa ne bayan matakin da jam'iyyar PDP mai adawa ta dauka game da takarar shugaban kasa kan zaɓen 2027 da ke tafe.
A ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025 jam'iyyar PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa (NEC) a birnin tarayya Abuja.
A taron, shugabannin PDP sun warware wasu daga cikin batutuwan da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu ciki har da batun tikitin takarar shugaban kasa.
Jam'iyyar ta amince da ba Kudancin Najeriya takarar shugaban kasa a zaben 2027 tare da tabbatar da kujerar shugaban PDP ga Arewa.

Source: Twitter
Abin da PDP ta ce kan dawowar Jonathan
Kakakin PDP ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan har yanzu mamba ne na jam'iyyar, Punch ta ruwaito.
Ya tabbatar da cewa Jonathan bai fice daga jam’iyya ba, amma ya ce ba zai yi magana kan Peter Obi ba saboda ba ya cikin PDP.
Ya ce:
“Ina tabbatar da cewa Jonathan har yanzu mamba ne saboda bai yi murabus ba."
Ya ce ba daidai ba ne ya yi sharhi kan Obi, amma ya jaddada cewa PDP na da mutane masu cancanta da kwarewa a yanzu.

Kara karanta wannan
"An makara": Hadimin Wike ya hango kuskure kan matakin PDP na kai tikitin takara Kudu
Ologunagba ya yabawa Gwamna Seyi Makinde, inda ya bayyana shi da jajirtaccen dan PDP saboda kwarewarsa da nasarorin da ya samu a jihar Oyo.
Ya kara da cewa:
“A bayyane yake, Makinde na daga cikin mutanen da za su iya hada kan Najeriya, kuma mutane suna ganin alherinsa.”
Ya kara da cewa PDP na alfahari da gwamnoni masu aiki tukuru, da kuma fitattun ’yan Najeriya da suka cancanta su jagoranci kasar.
Sanata ya magantu kan takarar Jonathan a PDP
A wani labarin mai kama da wannan, maganganu sun yiwa kan yiwuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi takara a zaben da za a yi shekarar 2027.
Sanatan PDP daga jihar Benue, Abba Moro, ya yi tsokaci kan yiwuwar Jonathan ya yi takara a karkashin jam'iyyar PDP.
Hakazalika, ya ce wasu jiga-jigan PDP sun fara sanya labule da Peter Obi don ya dawo babbar jam'iyyar mai adawa a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
