Dele Momodu: Yadda Wike da Tinubu Su ka Kawo Tsarin Miƙa Mulki Kudu a PDP

Dele Momodu: Yadda Wike da Tinubu Su ka Kawo Tsarin Miƙa Mulki Kudu a PDP

  • Jigo a ADC, Dele Momodu ya zargi PDP da yin mummunan kuskure wajen miƙa takarar shugaban ƙasa na 2027 ga Kudu
  • Ya ce wannan shiri ba wani abu ba ne face dabarar Nyesom Wike da APC don tabbatar da sake zaɓen Bola Tinubu a 2027
  • Dele Momodu ya bayyana cewa PDP ta mika kanta ga APC, yana mai kira kada jam’iyyar ta ci gaba da ruɗar ’yan Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT, Abuja – Ɗan siyasa kuma mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, ya caccaki jam’iyyar PDP kan yanke shawarar ware tikitin shugaban ƙasa na 2027 ga yankin Kudu.

Ya bayyana cewa wannan wani ƙagaggen shiri ne da APC, Bola Tinubu da Nyesom Wike suka samar.

Kara karanta wannan

PDP: Gwamnan Bauchi ya faɗi dalilin miƙa tikitin takarar shugaban ƙasa ga Kudu

Dele Momodu ya caccaki PDP
Hoton Dele Momodu tare da Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan ma kunshe a cikin sanarwar da Cif Dele Momodu ya fitar a ranar Talata.

Dele Momodu ya tausayawa jam'iyyar PDP

Punch ta wallafa cewa Dele Momodu ya zargi PDP da kashe kanga saboda rungumar tsarin magoya bayan APC a cikin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa:

"Jiya ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun Afrika, wacce ke cikin matsala, ta bindige kashe kanta."
"Abin takaici shi ne ganin manyan ’yan siyasa suna taya kansu murna kan wannan mummunan kuskure.”

Dele Momodu ya caccaki Wike, Tinubu

Cif Dele Momodu ya danganta wannan tsarin kai tsaye da tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa:

"Wanene bai san cewa aikin Wike ne, amma murya ta Tinubu ba? Wike yana ba gwamnoni umarni, kuma suna kasa tsayawa tsayin daka su bijire."
"Mutumin da ya ƙi tsarin karɓa-karɓa a 2022, har ma ya nemi zama mataimakin ɗan takara ga ɗan Arewa, shi ne yanzu ya fi kowa ihu cewa sai Kudu ta karɓi mulki a 2027.”

Kara karanta wannan

'APC da PDP sun tafka kuskure, da yiwuwar su sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027'

Dele Momodu ya caccaki Wike
H-D: Hoton Dele Momodu, Nyesom Wike Hoto: Dele Momodu/Nyesom Ezenwo
Source: Facebook

Ya ci gaba da cewa PDP ta fitar da tsarin ne domin taimaka wa Tinubu a 2027.

Dele Momodu ya ce:

“Ya kamata su fito fili su ce Tinubu shi ne ɗan takarar hadin gwiwa na APC da PDP. Kada su ci gaba da ruɗar mutane. Babu wani abu da zai hana Wike amfani da tsarin PDP don Tinubu ya ci zaɓe. Wannan shiri ne da aka riga aka gama.”

Ya kuma zargi PDP da yi domin ganin idanun mutane, inda ya tuna da tarihi:

“Ina suka kasance lokacin da Umaru Musa Yar’Adua ya rasu, kuma babu wanda ya yi jayayya cewa sai Arewa ta ci gaba bayan Jonathan ya karɓa? Jonathan ma da bai sha kaye hannun Buhari ba, da ya yi shekaru tara a mulki. Ina suka kasance lokacin da Tinubu ya tsaya da tikitin Musulmi/Musulmi?"

Gwamna ya faɗi dalilin ba Kudu takarar PDP

A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana dalilin da ya sa jam’iyyar PDP ta amince da ba Kudancin Najeriya tikitin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

Ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na tsarin karɓa-karɓa da kuma sake fasalin jam’iyyar kafin zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe domin su fito da kwarinsu.

Kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP ya gudanar da taro a Abuja, inda aka tabbatar da Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban jam’iyya da sauran tsare-tsare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng