Bayan kai Tikitin Takarar PDP Kudu, Sanata Ya Fadi Shirin Jam'iyyar kan Jonathan da Peter Obi

Bayan kai Tikitin Takarar PDP Kudu, Sanata Ya Fadi Shirin Jam'iyyar kan Jonathan da Peter Obi

  • Ana ta maganganu kan yiwuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi takara a zaben da za a yi shekarar 2027
  • Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, ya yi tsokaci kan yiwuwar Jonathan ya yi takara a karkashin jam'iyyar PDP
  • Hakazalika, ya ce wasu jiga-jigan PDP sun fara sanya labule da Peter Obi don ya dawo babbar jam'iyyar mai adawa a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya yi magana kan yiwuwar takarar Goodluck Jonathan da Peter Obi a zaben 2023.

Sanata Abba Moro ya yi nuni da yiwuwar Peter Obi da Goodluck Jonathan su koma jam’iyyar PDP, don su shiga takarar shugaban kasa.

Sanata Abba Moro ya yi magana kan Jonathan da Peter Obi
Hotunan Peter Obi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Shugaban marasa rinjayen na majalisar dattawa, Abba Moro, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Talata, 26 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

"Mun yi nadama": Sanata ya fadi kuskuren PDP kan Atiku a zaben 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Moro kan Goodluck Jonathan da Peter Obi

Sanata Abba Moro ya ce ana ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar dawowar su cikin babbar jam’iyyar ta adawa.

"A yayin shirye-shiryenmu na 2027, na san wasu mutane suna tattaunawa da Peter Obi suna cewa, ‘Kai, dawo gida, ga abin da muke shirin yi, idan ka dawo kana da damar zama ɗan takara'."

- Sanata Abba Moro

Da aka tambaye shi kan yiwuwar tsohon shugaban kasa Jonathan ya dawo cikin PDP, Sanata Abba Moro mai wakiltar Benue ta Kudu ya ce:

"Wasu mutane suna tattaunawa da tsohon shugaban kasa domin ya fito takara. Wannan abu wanda zai iya yiwuwa."

Jonathan ya mulki Najeriya a 2010-2015

Goodluck Jonathan ya yi mulki a karkashin jam’iyyar PDP daga shekarar 2010 zuwa 2015.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya karɓi mulki daga hannun maigidansa, Alhaji Umaru Musa Yar’Adua, bayan rasuwar shi a shekarar 2010.

Kara karanta wannan

PDP ta samu koma baya, tsohon sanatan Kebbi ya fice daga jam'iyyar

Jonathan ya tsaya takara karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2011 inda aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Sai dai kuma a 2015 ya yi rashin nasara a hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda hakan ya sanya shi zama shugaban kasa na farko da ya sha kaye a zaɓe tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999.

Tun daga wannan lokaci, Jonathan ya rage shiga harkokin siyasa kuma bai halartar tarurrukan PDP.

Ana kira ga Jonathan ya fito takara a 2027
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Sai dai akwai kiraye-kirayen da ake yi masa ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Duk da haka, Jonathan bai bayyana niyyarsa ba ko ya nuna sha’awar komawa kujerar da ya bari a 2015 ba. Haka kuma, bai taɓa sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a hukumance ba.

Sanata Moro ya ce PDP ta yi kuskure

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, ya ce PDP ta yi kuskure kan Atiku Abubakar a 2023.

Sanata Abba Moro ya bayyana cewa jam'iyyar ta yi nadamar tsayar da Atiku a matsayin dan takararta na zaben shugaban kasa.

Ya bayyana cewa bai kamata jam'iyyar ta tsayar da Atiku a matsayin dan takara ba, inda ya nuna cewa wannan kuskuren ne ya sanya ta fadi zaben 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng