PDP: Gwamnan Bauchi Ya Faɗi Dalilin Mika Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa ga Kudu

PDP: Gwamnan Bauchi Ya Faɗi Dalilin Mika Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa ga Kudu

  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana dalilin PDP ta na mika tikitin shugaban ƙasa na 2027 ga Kudancin Najeriya
  • Mai girma gwamnan ya ce wannan matakin karɓa-karɓa zai karfafa PDP a yayin tunkarar babban zaɓen 2027 da ke zuwa
  • Gwamna Bala Mohammed ya jaddada cewa siyasa sadaukarwa ce da haɗin gwiwa don samun ci gaban ƙasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi –Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana dalilin da ya sa jam’iyyar PDP ta amince da ba Kudancin Najeriya tikitin shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana haka ne bayan PDP ta tabbatar da fito da ɗan takararta da zai kara da APC daga Kudu.

PDP ta mika tikitin takarar 2027 ga Kudu
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Muhammad a yayin wani taro Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa a ranar Litinin ne kwamitin zartarwa na ƙasa na PDP ya gudanar da taro a Abuja, inda ya tabbatar da Iliya Damagum a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

PDP ta mika tikitin shugaban kasa zuwa Kudu

Jaridar Punch ta wallafa cewa Bala Mohammed ya ce wannan tsarin karba wani ɓangare ne na sake fasalin jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.

Ya ce:

"Na gamsu da wannan tsari kuma dabara ce da za ta kai mu ga ci."
"Shawara ce da kowa da kowa ya amince da ita domin a ci gaba da tsarin karɓa-karɓa domin miƙa ta ga Kudancin ƙasar nan, wannan zai ƙara karfafa haɗin kai."

Ya bayyana cewa tsarin zai ba PDP damar kara wa da APC a babban zaɓen 2027 da ke tafe.

Gwamnan jihar Bauchi, Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Hoton gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Twitter

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi kira ga ‘yan siyasa da su ajiye son zuciya wajen neman muƙami, inda ya ce manufar siyasa ita ce sadaukarwa don amfanar jama’a baki ɗaya.

Ya ce:

“Siyasa ba wai ta son rai bace. Komai na buƙatar sadaukarwa, ba son kai ba. Ya kamata mu yi rayuwa mu bar wasu ma su rayu, mu kuma sani cewa iko daga wurin Allah yake."

Kara karanta wannan

Jigon APC ya hango kuskuren PDP, ya faɗi yadda hakan zai taimaki Tinubu a 2027

Ya ƙara da cewa gwamnonin PDP, kwamitin zartarwa na ƙasa da majalisar amintattu sun haɗa kai domin tabbatar da cewa jam’iyyar ta kai ga ci.

Ya ce haɗin kan da su ka zai haifar da ɗa mai ido wajen ba PDP damar sake fitowa da ƙarfi a matsayin zaɓi ga ‘yan Najeriya a shekarar 2027.

Jam'iyyar PDP ta koka a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Kaduna ta bayyana damuwarta kan tsare ‘yar takararta a zaɓen cike gurbin kujerar Chikun/Kajuru.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Sir Edward Percy Masha, ne ya bayyana haka yayin hira da manema labarai a Kaduna, inda ya zargi gwamnati da takure ƴan adawa.

PDP ta bayyana cewa ƴar takararta a kujerar majalisar wakilai, Princess Esther Ashivelli Dawaki, tare da daraktan yaƙin neman zaɓenta, Shehu Fatangi na hannun EFCC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng