'APC da PDP Sun Tafka Kuskure, da Yiwuwar Su Sha Kaye a Zaben Shugaban Kasar 2027'
- Wani masanin siyasa, Farfesa K’tso Nghargbu ya ce jam'iyyun APC da na PDP na iya faduwa a zaben shugaban kasar 2027 mai zuwa
- Nghargbu, wanda ke fafutukar ganin an ba yankin Arewa ta Tsakiya damar mulkin kasa, ya ce manyan jam'iyyun sun danawa kansu tarko
- Ya ce APC da PDP sun yi watsi da Arewa a batun takarar shugaban kasa kuma hakan babbar illa ce ga nasarar da suke fatan samu a 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Masana siyasa sun fara hasashen yadda zaben shugaban kasa na 2027 zai kaya duba da yadda jam'iyyun siyasa suka fara rabon inda za su mika takara.
Wani masanin siyasa kuma jagoran masu fafutukar ganin an ba wa yankin Arewa ta Tsakiya damar mulki, Farfesa K’tso Nghargbu ya hango faduwar APC da PDP a 2027.

Source: Facebook
Wane kuskure PDP da APC suka yi?
Ya ce APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa PDP na iya shan kasa a zaɓen 2027 saboda watsi da yankin Arewa tare da miƙa takararsu ga yankin Kudu, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba, wasu shugabannin APC sun riga sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2027, haka kuma PDP ta ware tikiti ga yankin Kudu.
Sai dai sauran manyan jam’iyyu kamar ADC, LP da SDP ba su bayyana tsarin rabon tikitinsu ba tukuna.
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Talata, Farfesa Nghargbu ya ce cire yankin Arewa baki ɗaya da APC da PDP suka yi tamkar suna yakar kansu ne.
Ya ce idan ADC ta tsayar da ɗan takara daga Arewa, musamman Arewa ta Tsakiya, za ta iya lashe kujerar shugaban ƙasa a 2027 inji rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan
'Lokaci ya yi da za a dauki mataki,' ACF ta shiga takaicin yadda ake zubar da jinin 'yan Arewa
Masani ya nemi a ba Arewa ta Tsakiya dama
“Duk wata jam’iyya da ba za ta ba Arewa, musamman Arewa ta Tsakiya, tikitin shugaban ƙasa ba, to ta shirya rasa ƙuri’un mutanen yankin.
“Duka yankunan Arewa za su zauna su yanke shawarar wanda za su marawa baya. Burinmu shi ne a samu kyakkyawan shugabanci a kasa, wanda zai samar da zaman lafiya, adalci da gaskiya.
“Kuma muna kara jaddada cewa, yankin da aka hana mulki tun daga 1960 har yau, shi ne mafi cancanta a ba shi wannan damar a yanzu.
- in ji Farfesa K’tso Nghargbu.

Source: Facebook
Jam'iyyar ADC za ta iya lashe zaben 2027?
Game da batun ko jam'iyyar hadaka, ADC zata iya samun nasara a 2027, Nghargbu ya ce:
"Amsar tambayar ku a fili take, idan ADC ta tsayar da ɗan takara daga Arewa, kuma Arewa ta fito da ƙuri’unta gaba daya, to ba shakka za ta yi nasara.”
Daga cikin wadanda suke fatan samun tikitin jam'iyyar ADC a zaben shugaban kasa mai zuwa akwai mutanen yankin na Arewa irinsu Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan
'Karshen APC ya zo,' Gwamnonin PDP sun faɗi abin zai hana jam'iyya mai mulki sake cin zaɓe
ADC ta shawo kan Atiku, Obi da Amaechi
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar ADC ya bayyana cewa babu abin da zai raba manyan jagororin adawa, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rotimi Amaechi.
Jam'iyyar hadakar ta ce duka manyan jagororinta sun amince za su yi aiki tare domin kawo karshen mulkin APC a zaben 2027.
ADC na ci gaba da tattaunawa kan ko za ta ba wani yanki tikitin takarar shugaban kasa ko kuma za ta bar kofa a bude ga kowane dan kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
