PDP Ta Kara Birkicewa, 'Yan Majalisa 2 Sun Fice daga Jam'iyyar, Sun Koma APC

PDP Ta Kara Birkicewa, 'Yan Majalisa 2 Sun Fice daga Jam'iyyar, Sun Koma APC

  • ’Yan majalisar jihar Ondo biyu, Felix Afe da Tope Agbulu, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC, jam'iyya mai rinaye a majalisar
  • Sauya shekar ya bai wa APC rinjaye mai ƙarfi a majalisar Ondo, inda yanzu take da mambobi 24 yayin da PDP ke da 2 kacal
  • Bayan karanta wasikar sauya shekar, majalisar ta bukaci gwamnatin jihar ta fara biyan sabon albashin ma’aikatan majalisa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ondo - ’Yan majalisar jihar Ondo guda biyu da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Felix Afe da Tope Agbulu, sun koma jam’iyyar APC a ranar Talata.

Felix Afe yana wakiltar mazabar Akoko ta Arewa maso Yamma 2, yayin da Tope Agbulu ke wakiltar mazabar Akoko ta Kudu maso Yamma 2 a majalisar.

Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Ondo sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Hoton ginin majalisar dokokin jihar Ondo da ke birnin Akure. Hoto: @OndoAssembly
Source: Twitter

Ondo: 'Yan majalisar PDP sun koma APC

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

Kakakin majalisar, Benjamin Jayeola, ne ya karanta wasikun sauya shekar da ’yan majalisar suka aika wa majalisar, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dukkanin 'yan majalisar biyu sun ce rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar PDP a jihar ne ya sa suka yanke shawarar sauya sheka.

Felix Afe ya bayyana cewa ya yi shawara mai zurfi da 'yan mazaɓarsa da kuma manyan jagorori kafin ya yanke shawarar barin PDP, yana mai cewa shiga APC zai ba shi damar kawo ƙarin romon dimokuraɗiyya ga mutanensa.

Shi ma Agbulu ya ce APC ita ce mafi inganci wajen hidimta wa mazaɓarsa, yana mai gode wa PDP bisa goyon bayan da ta bashi lokacin da yake a jam’iyyar.

Batun sabon tsarin albashin ma’aikata

A cewar rahoton NAN, da wannan sauya sheka, APC ta samu mambobi 24 daga cikin 26 a majalisar, yayin da PDP ke da mambobi biyu kacal.

Tun da farko, majalisar ta umarci gwamnatin jihar ta aiwatar da sabon tsarin albashi na ma’aikatan majalisu (CONLESS) ga ma’aikatan majalisar jihar.

Ƙungiyar ma’aikatan majalisar, PASAN reshen Ondo, ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 21 don aiwatar da tsarin albashin.

Kara karanta wannan

APC ta dakatar da babban jami'in gwamnati saboda aikata zunubai masu girma

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Olatunji Oshati, ya bayyana cewa rashin aiwatar da tsarin albashin ya zama batun da ya shafi jama’a, inda ya ce majalisar ta ɗauki nauyin shiga tsakani.

Ya roƙi Gwamna Lucky Aiyedatiwa da ya biya buƙatun ma’aikatan majalisar, yana mai cewa sauran jihohin Kudu maso Yamma duk sun aiwatar da tsarin.

Majalia ta roki Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma'aikatan majalisar Ondo.
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa yana gabatar da jawabi a wani taro da aka yi a Akure. Hoto: @LuckyAiyedatiwa
Source: Facebook

An lallashi ma'aikatan majalisa kan albashi

Olatunji Oshati ya kuma roƙi ma’aikatan majalisar da su ƙara haƙuri su bar majalisar jihar ta shiga tsakani domin a sami maslaha cikin lumana.

Shi ma kakakin majalisar, Olamide Oladiji, ya ja hankalin ma’aikatan da kada su ɗauki doka a hannunsu, ya kuma yaba musu bisa haƙurinsu, tare da tabbatar da cewa majalisar za ta tattauna da gwamna domin nemo mafita.

Oladiji ya ce aiwatar da sabon tsarin albashin zai ƙara wa ma’aikatan ƙwarin gwiwar yin aiki mai inganci, tare da tabbatar musu cewa majalisar za ta ci gaba da kare muradunsu.

Shugabanni 2 sun yi murabus a majalisar Ondo

A wani labari, mun ruwaito cewa, majalisar jihar Ondo ta yi wasu ƴan sauye-sauye tsakanin shugabanninta a ranar Talata, 3 ga watan Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

APC ta shiga matsala, magoya bayan jam'iyyar 50,000 sun sauya sheka zuwa ADC a Sokoto

Mataimakin kakakin majalisa, Abayomi Akinruntan, da shugaban masu rinjaye, Emmanuel Ogunmolasuyi sun miƙa takardar ajiye muƙamansu.

Shugabannin biyu sun yi murbaus ne domin mutunta yarjejeniyar raba muƙamai, inda ƴan majalisar suka zaɓi wadanda suka maye gurbinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com