'Na Yi Mulkin Gaskiya': Ganduje Ya Yi Zazzafan Martani ga Gwamna Abba kan Zarge Zarge

'Na Yi Mulkin Gaskiya': Ganduje Ya Yi Zazzafan Martani ga Gwamna Abba kan Zarge Zarge

  • Kakakin tsohon shugaban APC, Muhammad Garba, ya yi martani ga gwamnatin jihar Kano kan tuhumar da aka jefa mata
  • Garba ya yi watsi da zarge-zargen gwamnatin Kano kan Abdullahi Umar Ganduje, yana kiran su da cewa siyasa ce kawai
  • Ya ce Ganduje ya yi mulki da gaskiya da amanar jama’a, inda ya gudanar da duk ayyuka cikin kasafin gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kakakin tsohon shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya yi martani ga gwamnatin jihar Kano.

Muhammad Garba ya yi Allah wadai da zarge-zargen da aka yi wa ubangidansa, yana cewa siyasa ce kawai.

Ganduje ya soki gwamnatin Abba Kabir kan zargin cin hanci
Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Facebook

A wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, Garba, wanda tsohon kwamishinan yada labarai ne a Kano, ya ce gwamnatin jihar ta kulla musu sharri, cewar Punch.

Kara karanta wannan

JIBWIS ta ƙalubanci masu cewa an yi wa Jingir ihu a Abuja, ta sanya kyautar kuɗi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin Abba Yusuf ta yi ƙoƙarin danganta Ganduje da almundahana, rashawa da kuma laifin kashe kuɗi ta hanyar ofishin daraktan tsare-tsare.

Zargin da Abba Kabir ya yiwa Ganduje

Hakan ya biyo bayan Abba Kabir Yusuf ya zargi Ganduje da kashe sama da Naira biliyan 20 a tsakanin Fabrairu da Mayu 2023 bayan APC ta sha kaye.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito ta karyata zargin cewa hadimisa ya wawure biliyoyi, yana mai bayyana shi a matsayin wani kullin siyasa da nufin bata gwamnatinsa.

Gwamnatin Kano ta kuma sake tunatar da mutane irin barnar da ake zargin tsohuwar gwamnati da ta gabata ta yi kafin ta bar mulki.

Ganduje ya yi martani kan zargin Abba Kabir

Sai dai mai magana da yawun ya dage cewa gwamnatin Ganduje ta kasance mai gaskiya da rikon amana, inda ya ce: “Ganduje ya kammala mulki da gaskiya.”

Kara karanta wannan

Bayani ya fito kan zargin hadimin Gwamna Abba da wawure Naira biliyan 6.5 daga asusun Kano

Ya ce danganta tsohon gwamnan da zarge-zargen rashawa siyasa ce kawai, domin a cewarsa, “wadannan labarai karya ne da aka kirkira.”

Garba ya ce:

“Tarihin Ganduje ya nuna hidima ga jihar Kano shekaru da dama ba tare da saba dokokin gwamnati ba.
"Wadannan labarai na bogi an tsara su ne don karkatar da hankali daga ainihin matsalolin mulki da ke addabar jama’a yanzu.”
An kare mulkin Abdullahi Ganduje a Kano
Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: All Progressives Congress.
Source: Twitter

Kakakin Ganduje ya kare mulkin mai gidansa

A kan batun filaye kuma, Garba ya ce Ganduje ya kafa tsarin kare kadarorin jama’a da kuma tabbatar da sahihin hanyar gudanarwar filaye.

Garba ya koka kan yadda wasu ke kokarin danganta matsalolin gwamnatin yanzu da Ganduje, yana cewa hakan ba gaskiya ba ne.

Ya yi kira ga jama’a, kafafen watsa labarai da ‘yan siyasa su daina amfani da sunan Ganduje don batanci da yaudara.

Gwamnatin Abba Kabir za ta horas da matasa

Kun ji cewa Hukumar fasahar sadarwa ta jihar Kano za ta haɗa kai da kungiyar KCI domin horas da matasa miliyan 1.5 wajen sana'o'i.

Kara karanta wannan

2027: An zaɓi Sule Lamiɗo domin takara da Jonathan? Tsohon gwamnan ya magantu

Shirin zai gudana tsakanin 2025 zuwa 2027, inda za a koyar da matasa a matakai daban-daban na ilimin zamani.

An riga an fara aikin gwaji inda matasa 150,000 suka shiga, yayin da sama da 1,000 suka kammala horo a cibiyoyi na jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.