Jigon APC Ya Hango Kuskuren PDP, Ya Faɗi yadda Hakan Zai Taimaki Tinubu a 2027

Jigon APC Ya Hango Kuskuren PDP, Ya Faɗi yadda Hakan Zai Taimaki Tinubu a 2027

  • Jigo a PDP, Gbenga Olawepo-Hashim ya soki matakin mika mulki Kudu, ya ce hakan taimakon Bola Tinubu ne a 2027
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana cewa PDP ba ta taɓa hana kowace jiha daga takarar shugaban ƙasa ba
  • Hakan ya biyo bayan matakin PDP na tura tikitin dan takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu domin wa'adin shekaru hudu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi magana kan tsarin karba-karba.

Olawepo-Hashim ya soki tsarin jam'iyyar na tura tikitin shugabancin ƙasa zuwa Kudancin Najeriya.

Jigon PDP ya soki matakin kai tikitin takarar shugaban kasa Kudu
Jigon PDP, Gbenga Olawepo-Hashim da shugaban jam'iyyar, Umar Damagum. Hoto: People's Democratic Party.
Source: Twitter

Takarar shugaban kasa: Jigon PDP ya soki jam'iyyar

A hirarsa da Channels TV bayan taron NEC na PDP a Abuja, ya gargadi cewa hakan tamkar amincewa da tazarcen Bola Tinubu ne.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olawepo-Hashim ya ce wannan mataki ba shi da tarihi a PDP tun farko domin babu adalci a ciki ko kadan.

'Dan siyasar ya yi nuni da cewa matakin zai raunana damar PDP ta fitar da ɗan takarar da zai iya fafatawa a 2027.

Ya bayyana cewa:

“Mika takarar shugabancin ƙasa zuwa kudu tamkar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu ne, masu yaƙin neman wannan sune masu yi masa aiki.
"Wannan rabon shugabanci ya zama hanyar hana PDP samun nagartaccen ɗan takara. Wannan salon yaƙi ne don Tinubu ya samu sauƙin tazarce.”

Olawepo-Hashim ya jaddada cewa PDP ba ta taɓa hana kowace yanki daga takara ba, yana kawo misalan zaɓukan shekarar 1999 da 2003.

“A 1999 Obasanjo ya fafata da Rimi daga Arewa da Dr. Alex Ekwueme, a 2003 Obasanjo ya sake fafatawa da Gemade da Rimi.”

- Cewar Olawepo-Hashim

PDP ta gudanar da taron NEC a Abuja
Jiga-jigan PDP a taron NEC na 102 da aka yi Abuja. Hoto: People's Democratic Party.
Source: Twitter

Jigon jam'iyyar PDP ya gargadi kwamitin NEC

Jigon PDP ya yi gargadin cewa NEC ta yi babban kuskure, duk da cewa matakin ya samu goyon bayan rinjaye, amma hakan babbar matsala ce.

Kara karanta wannan

Surutu ya kare, PDP bayyana yankin da za ta dauko dan takarar shugaban kasa a 2027

Olawepo-Hashim ya ce rabon shugabanci na iya haifar da rikici a doka, yana cewa kundin tsarin mulki bai amince da wariyar yanki ba.

Ya ce:

“Dokar Najeriya ba ta yarda a takaita ɗan jam’iyya daga neman mukami saboda asalinsa ba. Wannan matsala ce ta kundin tsarin mulki.”

Olawepo-Hashim ya ce PDP ta fi wasu jam’iyyu bin tsarin dimokuradiyya, inda ake yin tarurrukan da muhawara a cikin gida.

Ya zargi cewa yaƙin neman mika tikitin zuwa Kudu yana da alaka da ‘yan PDP masu mara wa Bola Tinubu baya don tazarcen 2027.

PDP ta tura tikitin shugaban kasa zuwa Kudu

Kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa (NEC) a birnin tarayya Abuja.

A taron, shugabannin PDP sun warware wasu daga cikin batutun da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu ciki har da batun tikitin takarar shugaban kasa.

Jam'iyyar ta amince da ba Kudancin Najeriya takarar shugaban kasa a zaben 2027 tare da tabbatar da kujerar shugaban PDP ga Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.