Bayani Ya Fito kan Zargin Hadimin Gwamna Abba da Wawure Naira Biliyan 6.5 daga Asusun Kano
- A 'yan kwanakin nan, an zargi hadimin gwamnan Kano da karkatar da kudi har Naira biliyan 6.5 daga asusun gwamnatin jihar
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito ta karyata zargin, yana mai bayyana shi a matsayin wani kullin siyasa da nufin bata gwamnatinsa
- Gwamnatin Kano ta kuma sake tunatar da mutane irin barnar da ake zargin tsohuwar gwamnati da ta gabata ta yi kafin ta bar mulki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin Kano ta musanta zargin cewa wani hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wawashe ko cire kudi har Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar.
Ta bayyana cewa wannan zargi karya ne domin duk wasu kudi da za su yi yawo tsakanin ma'aikatu da ofishin gwamnati su na tafiya ne bisa tsarin dokar kasafin kudi.

Source: Twitter
Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature D-Tofa ne ya yi wannan bayani a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yau Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shin hadimin gwamnan Kano ya wawure N6.5bn?
Sanusi Bature D-Tofa ya ce rahoton da jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ta wallafa a ranar 22 ga Agusta, 2025, na zargin hadimin gwamna da almundahana karya ce marar tushe.
Malam Sanusi Bature ya bayyana cewa duk da batun yana gaban kotu, amma gwamnati tana bukatar fayyace wa jama’a yadda ofishin kula tsare-tsaren gwamna ke aiki.
Ya ce dukkan kudaden da ake fitarwa zuwa ma’aikatun gwamnati ana yin su ne cikin tsarin kasafin kudi da dokoki, kuma babu wani jami’i da ke da ikon amfani da kudi ba tare da amincewar gwamnati ba.
Yadda mai tsara ayyukan gwamna ke aiki
Sanarwar ta kara da cewa ofishin Protocol na Kano yana da alhakin gudanar da abubuwa masu muhimmanci da suka shafi jigilar baki, masauki, walwala da shirya tafiye-tafiyen gwamna a cikin gida da kasashen waje.
Sanusi Bature ya ce aikinsu yana da alaka da manyan bak’i kamar ministoci, wakilan kasashen waje da ma jama’a da gwamna ke bai wa kulawa ta musamman.
Saboda haka, a cewarsa, yana gudanar da manyan harkokin kudi amma duk da haka a bisa doka da tsarin gwamnati.
"Zargin da ake yi wa shugaban ofishin tsare-tsaren gwamna, Abdullahi Ibrahim Rogo, bita da kulli ne na siyasa don bata sunan gwamnati," in ji shi.

Source: Facebook
Gwamnatin Kano ta kara tabo Ganduje
Gwamnatin Kano ta kuma yi nuni da cewa gwamnatin da ta gabata ta APC karkashin Abdullahi Umar Ganduje ta yi almubazzaranci da kudi fiye da Naira biliyan 20 a cikin watanni uku kafin barin mulki
Sanarwar ta kara jan hankalin jama’a da su yi watsi da irin wadannan zarge-zargen marasa tushe, tana mai cewa gwamnatin Abba ta himmatu wajen kare dukiyar jama’a da mulki cikin gaskiya.
Sai dai jawabin da aka fitar bai yi maganar zargin amfani da kwangilolin bogi wajen karkatar da kudin ko kuwa zargin da ake yi na fara maido wasu kudin ba.

Kara karanta wannan
ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027
Gwamnatin Kano za ta horar da matasa
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana sabon shirin horas da matasa miliyan 1.5 domin rage rashin aikin yi.
Wannan shiri zai gudana ne ƙarƙashin Hukumar Cigaban Fasahar Sadarwa ta jihar (KASITDA) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar KCI.
Manufar shirin ita ce samar da dama ga matasa domin su zama ginshiƙai a ci gaban fasaha da tattalin arziki, tare da bunkasa kwarewar da za ta taimaka wajen samar da ayyukan yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

