APC Ta Shiga Matsala, Magoya bayan Jam'iyyar 50,000 Sun Sauya Sheka zuwa ADC a Sokoto
- Dubunnan magoya bayan jam'iyya mai mulki ta APC a karamar hukumar Gada, a jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa ADC
- Wadanda suka sauya shekar sun ce sun bar APC saboda gazawar gwamnatinta wajen magance matsalar tsaro da tattali
- An ce fiye da mutum 50,000 suka shiga ADC, yayin da Sanata Abubakar Gada ya ce jam'iyyar hadaka za ta ceto Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Daruruwan mambobin jam’iyyar APC a karamar hukumar Gada ta jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC.
Wadanda suka sauya shekar, sun bayyana takaici kan yadda gwamnatin APC ta gaza wajen magance matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ta addabi al'umma.

Source: UGC
Sanata ya tarbi masu sauya sheka zuwa ADC
A ranar 24 ga Agusta, 2025, tsohon sanata kuma jigon jam’iyyar ADC, Sanata Abubakar Gada, ya karɓi wadanda suka sauya shekar a Gada, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wajen taron, Sanata Gada ya bayyana wannan mataki a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwa domin ceto Sokoto da Najeriya daga rashin kyakkyawan shugabanci.
“Mutanenmu sun ƙuduri aniyar kuɓutar da kansu da ƙasarsu daga mulkin shekaru na gwamnati mai ci, kowa na da yakinin ADC za ta kawo sauyi mai ma'ana.” inji Sanata Gada.
Ta'addanci ya durƙusar da tattalin Sokoto
Sanata Gada ya jaddada yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a yankin gabashin Sokoto, inda hare-haren ‘yan bindiga suka lalata harkar noma, wanda shi ne ginshikin tattalin arzikin yankin.
Sanata Gada ya ce:
“Rashin tsaro ya haifar da yunwa, talauci da rashin aikin yi. Mutanenmu ba za su iya yin noma cikin kwanciyar hankali ba yanzu.”
Masu sauya shekar sun maimaita waɗannan korafe-korafe a wajen taron, yayin da suka zargi APC da gazawa wajen fuskantar matsalolin, abin da ya sa suka koma ADC.
ADC na samun karɓuwa a jihar Sokoto
Rahoton jaridar The Sun ya nuna cewa fiye da mambobin APC 50,000 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC a Sokoto, lamarin da ya girgiza jam’iyya mai mulki.
Sanata Gada ya bayyana cewa an samar da hadakar 'yan adawa domin dawo da zaman lafiya da farfaɗo da harkar noma da bunkasa tattalin arziki.
“Kowane ɗan Najeriya na da haƙƙin tsaro da wadatuwar abinci. Jam'iyyar ADC ta zo don tabbatar da hakan,” inji Sanata Gada.

Source: Original
ADC za ta iya nasara a zaɓen 2027?
Da aka tambaye shi kan yiwuwar ADC ta kayar da APC mai mulki 2027, Sanata Gada ya ce ya dora yakininsa a kan ikon Allah.
“Mulki na Allah ne, ba na karfin jam'iyya ko gwamnati ba,” inji Sanata Gada, yana mai kira ga ‘yan Najeriya da su mara wa ADC don kawo sauyi a 2027.
Masu sharhi na ganin wannan sauya shekar a matsayin alamar raunin tasirin APC a Sokoto, inda ta saba da karfi a siyasa.
"APC kungiyar asiri ce' - Jigon PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Dakta Gbenga Olawepo-Hashim ya zargi APC da rashin akida, inda ya ce tsarin ta ya fi kama da na mulkin kama-karya.
Ya bayyana cewa APC ta jawo durkushewar tattalin arzikin Najeriya daga $570bn zuwa $300bn tare da karuwar matsalar tsaro.
Dakta Gbenga Hashim ya dage cewa PDP ce sahihiyar jam’iyyar dimokuraɗiyya, ya na mai neman ‘yan Najeriya su kawo sauyi a zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


