PDP Ta Samu Koma Baya, Tsohon Sanatan Kebbi Ya Fice daga Jam'iyyar
- Jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Kebbi ta samu nakasu bayan daga cikin manyan 'ya'yanta ya yi murabus
- Sanata Isa Galaudu wanda ya taba wakiltar Kebbi ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, ya sanar da ficewarsa daga PDP
- Tsohon dan takarar gwamnan na PDP a zaben 2019, ya ce daya daga cikin dalilinsa na fice daga jam'iyyar shi ne yadda abubuwa suka tabarbare
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Tsohon sanata mai wakiltar Kebbi ta Arewa a majalisar dattawa, Isa Galaudu, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP.
Isa Galaudu wanda shi ne dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2019, ya bayyana wannan mataki nasa ne a cikin wata wasika da ya rubuta mai ɗauke da kwanan watan ranar 20 ga watan Agusta, 2025.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce ya aika da wasikar ne ga shugaban jam'iyyar PDP na mazabar Augie ta Arewa a jihar Kebbi, Muhammadu Aliyu Danbuga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Isa Galaudu ya fice daga PDP
A cewar tsohon shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattawan, murabus ɗinsa daga jam’iyyar PDP ya fara aiki nan take, ba tare da wani jinkiri ba, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa ya dauki wannan matsaya ne bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a PDP a halin yanzu, da kuma sakamakon abin da ya bayyana rushewar jam’iyyar baki ɗaya.
"Na rubuto wannan wasika don sanar da kai cewa daga yau na yi murabus daga kasancewata ɗan jam’iyyar PDP. Wannan murabus ɗin ya fara aiki nan take."
"A bayyane yake cewa yanzu PDP tana ƙarƙashin ikon wasu ‘yan siyasa da ke cikin jam’iyyar da ke mulki a kasa.”
- Isa Galaudu
Isa Galaudu ya yi wakilci a matsayin Sanata daga 2011 zuwa 2015 a majalisar dattawa, inda ya wakilci Kebbi ta Arewa.
Haka kuma, ya taɓa yin aiki a matsayin ɗaya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.
Jam'iyyar PDP na fama da rikice-rikice
Sanarwar ficewar Isa Galaudu daga PDP ta zo a wani lokaci da ake ganin jam’iyyar tana fuskantar kalubale iri-iri daga cikin gida da kuma daga waje.

Source: Original
Yawancin masu sharhi sun bayyana cewa ficewar tsofaffin manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar Galaudu da wani babban koma baya ne ga makomar PDP, musamman a Arewacin Najeriya.
A daidai lokacin da siyasar kasar nan ke kara zafi wajen shirye-shiryen 2027, wannan murabus ɗin ya sake jefa tambayoyi kan yadda PDP za ta iya tsayawa da ƙafafunta da kuma ci gaba da kasancewa babbar jam’iyyar adawa.
Jam'iyyar ADC ta soki gwamnonin PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta ragargaji gwamnonin PDP kan yin taron siyasa a jihar Zamfara.
Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa taron da gwamnonin suka gudanar ya nuna rashin tausayi, duba da halin da Zamfara ke ciki na rashin tsaro.
Ta bayyana cewa ko kadan bai kamata gwamnonin na PDP su gudanar da taron siyasa a jihar Zamfara ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

