Tsohon Mataimakin Gwamna Ya Sauya Sheka, Ya Tabbatar da Ficewa daga PDP
- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia, Mista Ude Chukwu ya koma jam'iyyar LP makonni bayan ya raba gari da PDP
- Gwamna Alex Otti ne ya karbe shi hannu bibbiyu a wani taro da aka shirya a gidansa da ke karamar hukumar Ohafia a Abia
- Chukwu ya bayyana cewa salon mulkin Gwamnan na daya daga cikin abubuwan da suka jawo ra'ayinsa ya yanke shawarar shiga LP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Ude Chukwu, ya shiga jam’iyyar LP a hukumance a gidansa da ke garin Nkoro, karamar hukumar Ohafia.
Chukwu, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP kwanan nan, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Gwamna a karkashin tsohon Gwamna Okezie Ikpeazu da ya sauka a watan Mayu, 2023.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa wannan sauya sheka da ya yi zuwa LP mai mulkin jihar Abia ya bude sabon babi a siyasarsa tare da magoya bayansa, kamar yadda Punch ta rahoto
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Duka al'ummar Nkporo sun zo nan yau, wannan yana nuna cewa gaba daya jama'ar Nkporo sun koma jam'iyyar LP,” in ji Chukwu.
Me yasa tsohon mataimakin gwamna ya shiga LP?
Yayin da yake bayyana dalilinsa na sauya sheka, ya yabawa Gwamna Alex Otti bisa salon shugabancinsa, yana mai cewa:
“Na yanke shawarar hada kai da mai girma gwamna ne saboda yadda ya dauki mulki a matsayin wata manufa ta kashin kai.
"Ka yi matukar kokari. Yau muna alfahari da cewa mu ‘yan jihar Abia ne, daga yau an rufe babin PDP a jihar Abia domin ta mutu murus.”
- Ude Chukwu.
Gwamnan Abia ya rungume shi a LP
Da yake karbar Mista Chukwu a hukumance zuwa LP, Gwamna Otti ya yaba masa bisa jarumtarsa, yana mai bayyana shi a matsayin mutum “mai mutunta kowa da girmamawa.”
Ya kuma tabbatar da cewa ingancin ayyukan raya kasa da gwamnati ke aiwatarwa, ciki har da hanyar Nkporo da aka riga aka bude, za su yi daidai da na garuruwan Aba da Umuahia.

Kara karanta wannan
An dauki gwamna 1 a Najeriya, an ba shi lambar yabo ta 'Zabin Jama'a' a kasar Faransa
Shugaban jam’iyyar LP na jihar Abia, Sir Emmanuel Otti, ya ce dawowar Chukwu cikin jam’iyyar zai “zaburar da mutanen yankin ta yadda za su samu damammaki.”
Haka zalika, shugaban LP na karamar hukumar Ohafia, Godwin Kalu, ya yi alkawarin hada kan duka 'ya'yan LP domin kawo da ci gaba ga yankin.

Source: Facebook
Shugaban PDP ya sauya sheka zuwa LP
Bugu da kari, shugaban PDP na karamar hukumar, Egesi Eze Azu, ya sanar da cewa shi ma ya sauya sheka tare da Chukwu zuwa LP, cewar rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, tsohon mataimakin gwamna, Chukwu ya fice daga jam’iyyar PDP a ‘yan makonnin da suka gabata, yana mai bayyana “dalilai na kashin kai.”
PDP ta fusata da sauya shekar 'yan Majalisa 4
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta garzaya kotu tana neman a tsige sanatoci biyu da yan Majalisar Wakilai biyu saboda sun sauya sheka zuwa APC.
PDP ta shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja tana neman a ayyana cewa babu kowa a kujerun yan majalisar saboda sun karya doka.
Duka yan majalisar da PDP ta maka a Kotu sun fito ne daga jihar Osun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, yankin da Bola Tinubu ya fito.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
