2027: Atiku Ya ba da Kafa, Ya Faɗi Abin da Ya Sa Yake Takarar Shugaban Kasa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan takarar shugaban kasa a zaben 2027
- Atiku ya ce ba ya da bukatar zama shugaban kasa dole, abin da yake nema shi ne ganin Najeriya ta gyaru
- 'Dan siyasar ya bayyana hakan a wurin taron masu sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a Lagos da ke Kudancin Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar PDP a 2023, Atiku Abubakar ya magantu kan takararsa.
Atiku ya ce yana neman Najeriya ta inganta ne ba wai sai ya zama shugaban kasa ba dole ba.

Source: Facebook
Abin da Atiku ya fi so a Najeriya
Atiku ya bayyana hakan ne a wajen bikin maraba da sababbin wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC a Lagos ranar Asabar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku, wanda Farfesa Ola Olateju ya wakilta ya ce abin da yake nema shi ne gwamnati nagari, ba mulki na dole ba.
Ya ce:
“Ina da shirin gina Najeriya ta inganta. Ba game da zama shugaban kasa ba ne, amma gwamnati mai iya yi wa jama’a aiki."
Olateju ya kara da cewa ADC ba jam’iyya ba ce kawai, sai dai wata tafiya ta ’yan Najeriya masu neman canji da sabuwar hanya mai kyau.
Ya ce:
“Ba siyasa irin ta da ba, wannan farawa ne, Atiku yana jagorantar sabuwar tafiya domin kyakkyawan makomar Najeriya.”

Source: Facebook
Atiku ya jero matsalolin Najeriya a yanzu
Olateju ya jaddada cewa, manufarsu ba wai Atiku ko wani ya zama shugaban kasa dole ba, amma Najeriya ta samu ci gaba da kwanciyar hankali.
Atiku ya nuna cewa, matsalolin da Najeriya ke fama da su, musamman cire tallafin mai da tashin farashi, za su kau da shugabanci nagari.
Ya ce, Allah zai yi amfani da hadin kan mambobin wannan tafiya wajen kawo sauyi da kyakkyawar makoma ga al’ummar Najeriya baki daya.
Kan batun wanda zai samu tikitin ADC a 2027, Atiku ya ce jama’ar jam’iyyar ne kawai za su tantance ta hanyar sahihin zabe.
Manufar jam'iyyar ADC kan zaben 2027
Atiku ya ce ba dole ya zama shugaban kasa bane, ko Obi, amma duk wanda ya ci ya zama wakilin muradun jama’a, cewar The Guardian.
Sababbin wadanda suka sauya sheka sun hada da Dr. Abimbola Ogunkelu, tsofaffin shugabannin PDP na Legas, da wasu shugabannin matasa na jam’iyyar.
An tarbi wadannan sababbin mambobin ne ta manyan jagororin ADC ciki har da Rauf Aregbesola, Sanata Kolawole Ogunwale da George Ashiru, shugaban jam’iyyar na jihar.
Atiku ya fadi yadda aka daure mahaifinsa
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan wasu darussan da ya koya a rayuwarsa.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa saboda ƙin bari a sanya shi a makaranta, an taɓa ɗaure mahaifinsa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi bayani kan yadda ya taɓa tsallake rijiya da baya lokacin da aka yi yunƙurin hallaka shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

