Gwamna Abba Ya Dauko Hanyar Maida Kano 'Jagaba' a Yawan Masu Kada Kuri'a a 2027
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara shirin tara masu katin zabe akalla miliyan 10 kafin babban zaben 2027 da ke tafe a Kano
- Abba ya kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai zagaye kananan humomi 44 domin wayar da kan jama'a su yi rijistar zabe
- Kwamitin ya tabbatar wa gwamnan cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin duk wanda ya cancanta ya mallaki katin zaben a Kano kafin 2027
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da kwamiti na musamman mai mambobi 36 domin sa ido kan rajistar masu kada kuri’a a jihar.
Gwamna Abba ya umarci kwamitin ya tabbata cewa Kano ta hada masu rajistar zabe akalla miliyan 10 kafin kammala aikin ci gaba da rajistar masu kada kuri’a (CVR) na hukumar INEC.

Kara karanta wannan
ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Abba ya kaddamar da kwamitin ne a dakin taron majalisar zartarwa ta jihar Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Farouk Umar, ne ya wakilci mai girma gwamnan a wurin taron, wanda aka yi a fadar gwamnati.
Dalilin kafa kwamitin rijistar zabe a Kano
Ya bayyana cewa manufar kafa wannan kwamiti ita ce karfafa jama’ar Kano su fita su yi rajista domin samun damar kada kuri’a a zaben 2027.
Gwamna Abba Kabir ya ce:
“Katin zabe shi ne makamin dan kasa wajen sauya gwamnati. Ba za mu lamunci halin ko in kula ba. Duk wanda ya cancanci kada kuri’a ya tabbatar ya samu katinsa domin zaben shugabanni nagari.”
Ya kuma bayyana cewa Kano ta na da masu rajistar kada kuri'a sama da miliyan biyar, amma gwamnati na fatan kara samun miliyan biyar domin cimma burin miliyan 10.
Shawarar da Gwamna Abba ya ba sabon kwamitin

Kara karanta wannan
An dauki gwamna 1 a Najeriya, an ba shi lambar yabo ta 'Zabin Jama'a' a kasar Faransa
Ya shawarci kwamitin da su yi aiki da gaskiya da adalci, ba tare da nuna wariya ga kabila, addini ko matsayi ba, rahoton Guardian.
Haka kuma, gwamnan ya bukace su hada kai da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki don wayar da kan jama’a da kuma bin diddigin yadda aikin ke gudana.

Source: Facebook
Kwamitin da Abba ya kafa ya dauki alkawari
A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Kwamared Abdullahi Waiya, wanda shi ne Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, ya gode wa gwamnan bisa wannan amanar da ya ba su.
Ya ce kwamitin zai shirya tarukan wayar da kai da kuma zagaye kananan hukumomi 44 domin tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta ya yi rajista.
Ya kara da cewa, “Za mu yi aiki tukuru wajen ganin Kano ta zamo jagaba a yawan masu kada kuri’a a Najeriya.”
Gwamna Abba ya rantsar da sababbin hadimai
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Sa’idu Yahya a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta bullo da shirin afuwa ga 'yan daba, ta fadi wadanda za su amfana
An gudanar da rantsuwar ne a fadar gwamnatin Kano ranar Laraba, karkashin jagorancin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar, Barista Haruna Isah Dederi.
Har ila yau, gwamnan Kano ya rantsar da sababbin masu ba shi shawara har guda uku, inda ya bukaci su yi duk mai yiwuwa wajen kare mutun Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng