Datti Baba Ahmed: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Wa Hadakar 'Yan Adawa Tonon Silili
- 'Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya taso hadakar 'yan adawa a gaba
- Dr. Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa babu abin da 'yan hadakar suke yi sai yaudarar 'yan Najeriya
- Game da zaben shekarar 2027, Datti Baba-Ahmed ya bayyana aniyarsa ta sake yin takara tare da Peter Obi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya caccaki hadakar 'yan adawa.
Yusuf Datti Baba-Ahmed ya bayyana cewa haɗakar ’yan adawa da aka kafa ƙarƙashin jam’iyyar ADC na yaudarar ’yan Najeriya.

Source: Twitter
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Datti Baba-Ahmed ya ce kan hadaka?

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Ya bayyana cewa 'yan hadakar suna yaudarar 'yan Najeriya da cewa za su iya ceto kasar nan daga halin koma bayan da take ciki.
"Yaudararmu suke yi."
- Datti Baba-Ahmed
Yusuf Datti Baba-Ahmed shi ne ya tsaya tare da Peter Obi a matsayin mataimakin sa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu na APC ya lashe.
Baba-Ahmed na son sake takara tare da Obi
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasan na LP ya bayyana shirinsa na kasancewa tare da Peter Obi a matsayin abokin takara a zaɓen 2027.
Tuni dai Peter Obi, wanda ya bayyana sha’awarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, ya hade da jagororin haɗaka a ADC, kamar David Mark, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola.
Sai dai, Datti Baba-Ahmed ya ce yana fata tsohon gwamnan na Anambra, zai ci gaba da kasancewa a cikin LP, kuma ya tsaya takara da tutar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
"Ina cikin LP. Ni mutumin Peter Obi ne. Har yanzu ina so Peter Obi ya dawo cikin LP ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027."
- Datti Baba-Ahmed

Source: UGC
Datti Baba-Ahmed ya kara da cewa akwai mutane biyu ne kawai da zai yarda ya tsaya ya zama mataimakinsu.
“Na farko bai taɓa cewa komai ba. Na biyu shi ne Peter Obi. Ni kullum ina tare da Peter Obi har sai lokacin da ya yanke shawarar fasa takara."
- Yusuf Datti Baba-Ahmed
Peter Obi ya ragargaji Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu, kan shillawa zuwa kasashen waje.
Peter Obi ya bayyana cewa shugaban kasan bai damu da halin da 'yan Najeriya suke ciki ba, shiyasa yake yawan barin kasar nan tafiya wasu kasashen.
Ya bukaci Shugaba Tinubu da ya rika ziyartar jihohin Najeriya domin ganewa idonsa halin da mutane suke ciki, maimaikon zuwa kasashen wajen domin ba a zabe shi don ya zama dan yawon bude ido ba.
Asali: Legit.ng
