Mambobi 4 Sun Shiga Matsala Mai Girma da Suka Yi Yunkurin Tsige Kakakin Majalisa
- Majalisar dokokin jihar Benuwai ta gaggauta daukar mataki bayan jin kishin-kishin din cewa wasu mambobin na shirin tsige shugaban Majalisa
- A zaman yau Juma'a, 22 ga watan Agusta, 2025, an dakatar da yan majalisa hudu na tsawon watanni shida bisa zarginsu da hannu a kulla makircin
- Shugaban masu rinjaye ya ce wannan yunkuri na tsige kakakin Majalisar dokokin Benuwai na iya tayar da rikici da rudani a tsakaninsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Majalisar Dokokin Jihar Benuwai, a ranar Juma’a, ta dakatar da yan majalisa hudu daga aiki na tsawon watanni shida.
Majalisar ta dauki wannan mataki ne cikin gaggawa a zamanta na yau Juma'a, 22 ga watan Agusta, 2025 a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an dakatar da yan Majalisar ne bisa zarginsu da kulle-kullen tsige shigaban Majalisar dokokin jihar, Hon. Aondona Dajoh.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Majalisa 4 da aka dakatar a Benuwai
Yan Majalisar da aka dakatar sun hada da Hon. Alfred Beger, mamba mai wakiltar mazabar Makurdi ta Arewa da Hon. Terna Shimawua, mai wakiltar mazabar Kian.
Sauran sun hada da Hon. Cyril Ekong, mamba mai wakiltar mazabar Obi da kuma Hon. James Umoru, dan Majalisa mai wakiltar mazabar Apa, duka a Majalisar dokokin Benuwai.
Bisa ga bayanan da aka samu daga majalisar, wannan mataki ya biyo bayan zargin wasu mambobi da yunkurin tsige Shugaban Majalisar dokokin, Hon. Aondona Dajoh.
Me yasa aka dakatar da yan Majalisar 4?
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin yan Majalisar sun fara kulla yadda za su sauke shugaban nasu ne a daren ranar Alhamis a sirrince amma labarin ya fasu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon Saater Tiseer, ne ya gabatar da kudurin gaggawa inda ya bukaci a dakatar da wadannan mambobi hudu a zaman yau Juma'a.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi ya yi magana kan nada tsohon gwamna a matsayin Sarki mai daraja a Najeriya
Ya ce ya zama dole ya ladabtar da yan majalisar saboda yunkurin tada rikici da kawo rudani a cikin majalisar ba tare da wani dalili mai tushe ba.
A lokacin muhawara, Hon. Elias Audu (Gwer ta Gabas) da babban mai tsawatarwa, Peter Ipusu (Katsina-Ala ta Yamma), sun yi Allah wadai da abin da yan majalisar huɗu suka aikata tare da goyon bayan kudirin dakatarwa.

Source: Facebook
Majalisar Benuwai ta yi sauye-sauye
Bayan amincewa da kudurin, Kakakin Majalisar ya umarci sajan na Majalisa ya fitar da mambobin da aka dakatar daga zauren majalisar nan take, inji rahoton Daily Trust.
Kakakin majalisar ya kuma rushe dukkan kwamitoci sannan ya sanar da sababbin nade-nade, insa ya nada Elias Audu a matsayin mai magana da yawun majalisar,
Haka nan kuma ya nada Douglas Ackya a matsayin babban mai tsawatarwa da kuma Kennedy Angbo a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.
Gwamnan Benuwai ya sallami kwamishinoni
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya sallami dukkan kwamishinoninsa daga aiki a wani yunkuri na gyara Majalisar Zartarwa

Kara karanta wannan
INEC: 'Dan takara da ke daure a gidan yari ya lashe zaben dan majalisa a Najeriya
Sai dai bayan haka, Gwamna Alia na jam'iyyar APC ya naɗa Barista Moses Ataghera matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnati jihar Benuwai (CoS).
Kafin hawa wannan mukami, Barista Moses Atagher ya taba rike kwamishinan shari’a da kuma shugaban bankin FMB.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
