Yana Shirin Kawo wa Hadakar Adawa Tarnaki, Jam'iyyar ADC Ta Fatattaki 'Shugabanta'
- Jam’iyyar ADC a Gombe ta kori Nafiu Bala bayan ya ayyana kansa shugaban jam’iyyar na ƙasa bayan David Mark
- Haka kuma ta ladabtar da wasu manyan ADC uku da aka samu da rashin da’a da ƙoƙarin jawo rarrabuwar kawuna
- Shugaban ADC na Gombe Malam Auwal Abba Barde ya ce jam’iyyar ba za ta lamunci cin amana ko tawaye ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Jam’iyyar gamayar ’yan adawa ta ADC reshen jihar Gombe ta sanar da korar ɗaya daga cikin 'ya'yannta.
Matakin ya biyo bayan ikirarin da Nafi'u Bala ya yi cewa shi ne sabon shugaban jam’iyyar na kasa, tare da jayayya da jagorancin David Mark.

Source: Twitter
Jaridar Aminiya ta wallafa cewa shugaban ADC na jihar Gombe, Malam Auwal Abba Barde ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Gombe ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
'Akwai matsala a N70, 000,' Amurka ta fitar da rahoto kan mafi karancin albashin Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar ADC ka kori jigo a cikinta
Malam Auwal Abba Barde ya ce Nafi'u Bala ya wuce iyaka wajen keta tsarin jam’iyya da kuma yunkurin kawo rabuwar kai, abin da ya sa aka ɗauki matakin da ya dace.
Barde ya bayyana cewa Nafi'u ya ayyana kansa shugaban ƙasa na ADC ba tare da wani sahihin zaɓen jam’iyya ba.
Bayan haka kuma, ya sanar da sauke wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar a jihar, abin da ya haifar da rikici.
Ya ce an gayyaci Bala domin ya bayyana gaban kwamitin ladabtarwa na Nasarawo don kare kansa, amma ya ƙi amsa kiran.

Source: Facebook
Wannan rashin amsa ya sa aka ɗauki matakin kori da shi daga jam’iyyar gaba ɗaya bisa rashin biyayya da rashin da’a.
ADC ta ladabtar da wasu shugabanni 3
Barde ya ƙara da cewa a yayin da ake duba batun Bala, jam’iyyar ta kuma ladabtar da wasu manya guda uku.

Kara karanta wannan
'Dan APC ya firgita da hadaka, ya fadi yadda Atiku da Obi za su iya kifar da Tinubu
Sun haɗa da Mataimakin Shugaban Jiha, Nasiru Lawan; Sakataren Jiha, Danladi Ya’u; da Shugaban Matasa, Abdulkadir Sa’idu Digiri.
Jam'iyyar ta zargi jagororin uku da ayyukan da su ka saɓa wa manufofin ADC.
Shugaban ADC na Gombe ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta lamunci kowanne irin cin amanar jam’iyya ko rashin biyayya ba, tare da tabbatar ba.
Ya ce wannan mataki ya zama wajibi domin tabbatar da haɗin kai da karfi jam'iyyar yayin da ta ke shirin shiga babban zaɓen 2027.
2027: An yi hasashen kan jam'iyyar ADC
A baya mun wallafa cewa tsohon ɗan majalisar wakilai, Dr. Farah Dagogo, ya bayyana cewa hadakar jam’iyyar ADC na ƙara samun ƙarfi da karbuwa.
Ya ce soyayyar da mutane ke nuna wa ADC zai iya ba ta dama ta zama babbar barazana har ta kai ga lallasa jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓen 2027.
Dagogo ya yi kira ga magoya baya da sauran jam’iyyun adawa su haɗa kai, inda ya jaddada cewa da haɗin gwiwa ne kawai za a iya kayar da APC daga mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng