Tafiyar Kwankwaso Ta Girma, An Yi Taron 'Yan Kwankwasiyya a Birtaniya

Tafiyar Kwankwaso Ta Girma, An Yi Taron 'Yan Kwankwasiyya a Birtaniya

  • Ƙungiyar Kwankwasiyya ta reshen Biritaniya ta gudanar da taro domin ƙara yawan mambobi da ƙarfafa tsarin tafiyar
  • An bayyana cewa Kwankwasiyya ba ra’ayin siyasa kaɗai ba ce, illa wani salo na rayuwa da ya ginu kan gaskiya da sadaukarwa
  • Tafiyar ta samo asali daga jagorancin Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya kafa ginshiƙanta a kan ilimi da ci gaban al'umma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Britain -Reshen ƙungiyar Kwankwasiyya da ke Biritaniya ya gudanar da wani taro na musamman domin ƙarfafa alaka da jawo sababbin mambobi cikin tafiyar.

Ƙungiyar ta ce wannan mataki yana daga cikin shirye-shiryenta na tabbatar da cewa tsarin Kwankwasiyya ya ci gaba da zama abin koyi ga al’ummar Najeriya a gida da waje.

Taron da 'yan Kwankwasiyya suka gudanar a Birtaniya
Taron da 'yan Kwankwasiyya suka gudanar a Birtaniya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan taron ne a cikin wani sako da hadimin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.

Kara karanta wannan

Tallafin wankin koda: Gaskiya ta fito kan zargin Tinubu da ware Kano, jihohin Arewa 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi taron Kwankwasiyya a Birtaniya

'Yan Kwankwasiyya sun yi wani taro da Birtaniya domin karfafa hadin kai da jawo mutane cikin tafiyar su.

A wajen taron, Legit Hausa ta hango jama'a da suka hada da maza da mata, wasu na sanye da jar hula da ke nuna alamar tafiyar Kwankwasiyya.

Wasu 'yan Kwankwasiyya a Birtaniya
Wasu 'yan Kwankwasiyya a Birtaniya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Tarihin tafiyar Kwankwasiyya a Najeriya

A bayanan da aka wallafa a shafinta, Kwankwasiyya ta ce ita ba tafiyar siyasa ba ce kawai, illa wata tafiya da ta mamaye zukatan dubban mutane musamman a Arewacin Najeriya.

An kafa ta ne daga hangen nesa na Rabiu Musa Kwankwaso wajen samar da ilimi, ci gaban jama’a da jagoranci na gaskiya.

A ƙarƙashin tutar Kwankwasiyya, ɗalibai da dama sun samu tallafin karatu, al’ummomi da yawa sun samu sababbin hanyoyn rayuwai, makarantu, asibitoci da sauransu.

Ta haka ne tafiyar ke fatan canza tsarin shugabanci daga mai ci da gumin jama’a zuwa wanda ya ke fifita bukatun jama’a.

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

Tarihin jagoran tafiyar Kwankwasiyya

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi aiki a matsayin gwamnan Kano sau biyu, daga 1999–2003 da 2011–2015.

Ya kuma zama ministan tsaro na farko a 2003, bayan nan kuma ya zama ɗan majalisar dattawa daga Kano ta tsakiya.

A yayin mulkinsa, ya aiwatar da manyan ayyuka na ilimi da gine-gine, inda ya kafa makarantun sakandare da jami'a, ya gina hanyoyi da asibitoci, tare da ƙarfafa shirin tallafin karatu.

Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasa a Najeriya da suka yi takarar shugaban ƙasa a lokacin zaben 2023.

Yau tafiyar Kwankwasiyya ta wuce Kano, ta shiga wasu jihohin Najeriya tare da samun mabiya a ƙasashen waje ciki har da Biritaniya.

Ganduje ya dawo Najeriya daga Birtaniya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dawo Najeriya daga Birtaniya.

Abdullahi Umar Ganduje ya kasance daya daga cikin mabiya Kwankwasiyya kafin su raba hanya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Birtaniya ne kwanaki kadan bayan murabus da ya yi daga shugabancin jam'iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng