Sanatoci 2 da 'Yan Majalisar Wakilai 2 Sun Shiga Matsala bayan Ficewa daga PDP
- Jam'iyyar PDP ta garzaya kotu tana neman a tsige sanatoci biyu da yan Majalisar Wakilai biyu saboda sun sauya sheka zuwa APC
- A cewar PDP, abin da yan majalisar suka yi ya sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima
- Ta bukaci kotu ta umarci Majalisar Dattawa da ta Wakilan Tarayya su ayyana cewa babu kowa kan kujerun wadanda take kara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun - Jam’iyyar PDP ta fara kokarin bin hanyoyin doka wajen tsige yan Majalisar Tarayya hudu da suka fice daga cikinta zuwa APC a jihar Osun.
PDP ta shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja tana neman a ayyana cewa babu kowa a kujerun yan majalisar saboda sun karya dokar sauya sheka.

Kara karanta wannan
Dilolin kwaya 2 sun gamu da hukumar NDLEA, kotu ta yanke masu shekaru 10 a kurkuku

Source: Facebook
Sanatoci da yan majalisar da PDP ta kai kara
Rahoton Leadership ya nuna cewa wadanda PDP ta maka a kotun sun hada da sanatoci biyu da yan Majalisar Wakilan Tarayya guda biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisar da ake magana a kansu sun haɗa da:
1. Sanata Francis Adenigba Fadahunsi (Osun ta Gabas)
2. Sanata Olubiyi Oluwole Fadeyi (Osun ta Tsakiya)
3. Hon. Omirin Emmanuel Olusanya (Atakumosa East/West da Ilesa East/West)
4. Hon. Taofeek Abimbola Ajilesoro (Ife Central/East/North da South).
Abin da karar jam'iyyar PDP ta kunsa
Lauyan PDP, Rapheal Oyewole, ya shigar da ƙarar a madadin jam’iyyar, inda kowane ɗan majalisa daga cikin huɗun aka zayyano shi a matsayin wanda ake tuhuma na farko.
An ambaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio a matsayin wanda ake tuhuma na biyu a shari’ar da ta shafi sanata biyu.
Sai kuma Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya zama wanda ake tuhuma na biyu a shari’ar da ta shafi ‘yan majalisar wakilai biyu.
Haka kuma, an saka Majalisar Dokoki ta Tarayya (NASS), Magatakardan majalisa da hukumar INEC a matsayin wadanda ake tuhuma na uku zuwa na biyar, rahoton Punch.
Dalilin PDP na neman kwace kujerun 'yan Majalisar
PDP ta nemi kotu ta yi karin haske kan ko bisa sashe na 68(1)(g) na kundin tsarin mulki 1999, sanata ko ɗan majalisa na da hurumin ci gaba da rike kujerarsa bayan sauya sheƙa daga jam’iyyar da ya ci zabe kafin karewar wa’adinsa, idan babu rabuwar kai a cikinta.
Jam’iyyar PDP ta roƙi kotu ta ayyana cewa ci gaba da zama a kujerun majalisa da waɗannan ‘yan majalisa hudu ke yi bayan barin PDP ya saba wa kundin tsarin mulki.

Source: Twitter
PDP ta kuma bukaci kotu ta tilasta wa Akpabio da Abbas su bayyana cewa babu kowa a kujerun wadannan yan majalisa, sannan INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbi a mazabunsu.
Ta kuma roƙi kotu ta umarci magatakardan NASS ya dakatar da biyan su albashi, alawus da sauran hakkoki, tare da umartar waɗannan ‘yan majalisar su dawo da kudin da suka karba bayan barin PDP.

Kara karanta wannan
Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari
Rikicin PDP ya kai matsayin a sauya sheka?
A wani labarin, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya ce babu rabuwar kai na shugabanci a jam'iyyar PDP.
Abba Moro ya ce duk da akwai rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP amma dai ba ta rabe kamar yadda ake gani a wasu jam'iyyun adawa ba.
Ya jaddada cewa matsalolin da PDP ke fuskanta a yanzu sabani ne na ra’ayi da tsari wanda bai kai matsayin rabuwar kai da zai sa mutum ya sauya sheka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
