'Dan APC Ya Firgita da Hadaka, Ya Fadi Yadda Atiku da Obi za Su Iya Kifar da Tinubu

'Dan APC Ya Firgita da Hadaka, Ya Fadi Yadda Atiku da Obi za Su Iya Kifar da Tinubu

  • Wani babba a APC, Dominic Alancha ya yi gargadi jam'iyyarsa kan matsalar da za ta iya fada wa a zaɓen 2027 mai zuwa
  • Mista Alancha ya ce haɗuwar Atiku Abubakar da Peter Obi na iya jawo wa jam'iyyar asarar kujerar Shugaban Najeriya
  • Ya ce ci gaba da tsarin Muslim-Muslim ga Shugaba da Mataimaki zai zama makami da ƴan adawa za su yaƙi APC da shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wani jagora a jam'iyya mai mulki ta APC, Dominic Alancha, ya hango abin da zai kawo cikas ga muradinsu na ci gaba da mulkin Najeriya har bayan 2027.

Mista Alancha ya yi gargadi cewa haɗa karfi da karfe tsakanin Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben 2027 ka iya zama babban barazana ga jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Kashim: Wike ya fallasa dalilin da ya sa Babachir Lawan ke yawan sukar Bola Tinubu

Obi, Tinubu da Atiku
H-D: Peter Obi, Bola Tinubu da Atiku Abubakar Hoto: Mr. Peter Obi/Bayo Onanuga/Atiku Abubakar
Source: Facebook

Alancha ya bayyana hakan ne a hirar sa da Channels Television a shirin Politics Today, inda ya nuna cewa akwai jan aiki a gaban APC idan tana son ci gaba da mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagora a APC ya hango wa Tinubu matsala

The Cable ta ruwaito cewa Dominic Alancha ya na ganin idan Atiku da Obi suka yi yarjejeniya su fito a kan tikitin ɗaya, za su iya fitar da jam’iyyar APC daga fadar Shugaban Ƙasa.

Ya ce:

“A 2027, abubuwa ba lallai su kasance kamar a 2023 ba. Idan Peter Obi da Atiku suka iya daidaita kansu, su yi yarjejeniya a tsakaninsu, ina gaya muku hakan zai rage mana magoya baya.”

A zaben 2023 da aka yi, Bola Ahmed Tinubu na APC ne ya lashe shugabancin ƙasa da kuri’u 8,794,726, yayin da Atiku ya samu 6,984,520, Obi kuma ya zo na uku da 6,101,533.

'Dan APC ya magantu kan tikitin Muslim-Muslim

Kara karanta wannan

"Kan mage ya waye": Jam'iyyar PDP ta kada hantar APC, ta fadi abin da zai faru a 2027

Alancha, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Northern Ethnic Nationality Forum (NENF), ya shawarci Tinubu ya sauya tsarin Muslim-Muslim a 2027.

Ya ce rashin sauya Kashim Shettima yana iya babban makami ga 'yan adawa wajen neman kuri'ar ƴan Najeriya, kuma za su iya kai wa ga nasara.

Jonathan, tsohon shugaban ƙasa
Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

A cewarsa:

““Idan aka ci gaba da tsarin Muslim-Muslim, hakan zai zama barazana kuma zai rage mana magoya baya. Idan Obi da Atiku suka haɗa kai, muna magana ne kan kusan kuri’u miliyan 14 a kan kuri’unmu miliyan 8 daga zaben 2023.”

Ya kuma yi nuni da rade-radin yiwuwar dawowar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a zaben 2027, kuma wannan ma zai iya bai wa APC matsala.

A cewarsa, yanzu kamfen bai fara ba, amma idan aka shiga lokacin yaƙin zaɓe, matsalolin za su fito fili, don haka lokaci ne na shiri tun daga yanzu.

Ana zargin Minista da jawo wa APC asara

A baya, mun wallafa cewa wata ƙungiyar magoya bayaan APC ta danganta faduwar jam’iyya a zaben cike gurbi na mazabar Ibadan ta Arewa da guda daga cikin Ministocin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

An bukaci a kashe Bello Turji kamar Shekau duk da ya nemi ya Mika Wuya

Kungiyar ta ce rabuwar kai cikin jam’iyyar a jihar Oyo da kuma tasirin wani babban jigo—Ministan harkar makamashi, Cif Adebayo Adelabu ne su ka sa aka doke su.

A cikin sanarwar da mukaddashin shugaba da sakataren kungiyar—Alhaji Akindele Olatubosun da Taiwo Adeniyi—suka fitar sun zargi Ministan da jiji da Kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng