2027: Wike Ya Debo Ruwan Dafa Kansa kan Sukar Tsohon Ministan Buhari
- Minista babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fito ya ce Rotimi Amaechi, ba zai kai labari ba a zaben shugaban kasa na 2027
- Jigon APC a jihar Rivers, Cif Eze Chukwuemeka Eze, bai ji dadin wadannaan kalaman ba, wanda hakan ya sanya ya yiwa Wike martani
- Cif Eze Chukwuemeka ya bayyana cewa Wike ya yi kadan ya yanke makomar siyasar tsohon ministan sufuri watau Amaechi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi wa Nyesom Wike martani kan sukar tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.
Jigon na APC ya bayyana cewa makomar Chibuike Rotimi Amaechi, a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027 Allah ne kaɗai da kuma ’yan Najeriya za su yanke ba abokan hamayyar siyasa ba.

Source: Facebook
Eze Chukwuemeka Eze ya faɗi haka ne a matsayin martani bayan Wike ya ce Rotimi Amaechi ba zai kai labari ba a zaben 2027, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike dai ya bayyana cewa Amaechi ba zai iya samun tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a 2027 ba.
Wane martani jigon APC ya yi wa Wike?
Yayin kalubalantar wannan magana, Eze Chukwuemeka ya yi tambaya kan ko Wike ya zama “Allah ne ko kuma ɗan jam’iyyar ADC” da zai iya yanke makomar siyasar Amaechi.
"A wannan lamari, Allah ne kaɗai wanda kullum yake tsara makomar Amaechi a siyasa, shi ne zai kaddara makomarsa a shekarar 2027.”
- Cif Eze Chukwuemeka Eze
Ya kara da cewa wakilan jam’iyya ba mutum ɗaya ba, su ne za su tantance wanda zai ɗauki tutar jam'iyyar ADC a 2027.
Jigon na APC ya zargi Wike da abin da ya kira tsoron dawowar Amaechi a siyasa, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
An ambaci halayen Rotimi Amaechi
Eze ya kuma jaddada manyan ayyukan Amaechi a matsayin tsohon gwamnan jihar Rivers da ministan sufuri, inda ya bayyana shi a matsayin kwararren jagora mai karfin zuciya wajen yaki da cin hanci idan aka zaɓe shi shugaban kasa.

Source: Facebook
'Dan siyasar ya yi watsi da zarge-zargen da Wike ke yi kan sayar da injinan samar da wutar lantarki na Rivers a lokacin mulkin Amaechi, yana mai cewa an riga an fayyace batun kuma an rubuta shi a cikin kasafin kuɗin jihar na baya.
Ya jaddada cewa Amaechi har yanzu babban jigo ne a siyasa, wanda makomarsa ke hannun Allah da kuma ’yan Najeriya.
Jam'iyyar PDP ta nuna yatsa ga Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, ta nuna yatsa ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike.
PDP ta bayyana cewa babu wanda ya isa ya kafa mata sharadin abin da za ta yi, sabanin wanda yake a cikin kundin tsarin mulkinta.
Jam'iyyar ta bayyana hakan ne bayan Wike ya kafa sharudda wadanda yake so a cika kafin ya bari a samu zaman lafiya a PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
