"Ba Mu Ga Takarda ba," Rikicin APC Ya Dauki Sabon Salo bayan Dakatar da Sanata

"Ba Mu Ga Takarda ba," Rikicin APC Ya Dauki Sabon Salo bayan Dakatar da Sanata

  • Tsohon gwamnan Ogun kuma sanata mai ci, Gbenga Daniel ya ce har yanzu ba a aiko masa da takardar dakatarwa daga APC ba
  • Mai magana da yawun sanatan, Steve Oliyide ne ya sanar da hakan sa'o'i kadan bayan APC ta dakatar da Daniel da wani jigo, Kunle Folarin
  • Shugaban APC na jihar Ogun ya ce sun dakatar da jiga-jigan bisa rahoton kwamitin ladabtarwa na mazabunsu kan zarge-zargen da ake yi masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Rikicin da ya barke a jam'iyyar APC reshen jihar Ogun ya dauki sabon salo bayan dakatar da tsohon gwamna, Sanata Gbenga Daniel.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Steve Oliyide ya ce har yanzu babu wata takardar dakatarwa a hukumance da APC ta aikawa Sanatan Ogun ta Gabas.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnan Neja ya ce za su daina tura shanu Kudancin Najeriya

Sanatan Ogun ta Tsakiya, Gbenga Daniel.
Hoton tsohon gwamnan jihar Ogun, Gbenga Daniel wanda APC ta dakatar Hoto: Gbenga Daniel
Source: Twitter

Oliyide ya shaida wa Channels tv cewa har yanzun ba a ba su takarda a hukumance ba, a kafafen sada zumunta da jaridu kadai suka ji batun dakatarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ba a tura wa Sanatan Ogun ta Gabas wata wasiƙa ba da ke sanar da shi game da abin da ake zarginsa da shi da kuma dakatarwar da aka yi masa.

Meyasa APC ta dakatar da Sanata Gbenga Daniel

Wannan kalamai na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan jam'iyyar APC ta jihar Ogun ta sanar da dakatar da Sanata Daniel da wani mamba mai suna Kunle Folarin.

Mai magana da yawun jam’iyyar APC a jihar, Nuberu Olufemi, ya ce an ɗauki wannan mataki ne bisa zarginsu aikata ayyukan da suka sabawa jam’iyya da zagon kasa.

A cewarsa, sun yi haka ne domin a samu damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen da ake yi masu cikin gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a APC, an dakatar da tsohon gwamna kuma sanata mai ci

Shugaban APC ya yi karin haske kan lamarin

A wata sanarwa da shugaban APC na jihar Ogun, Yemi Sanusi ya fitar, ya ce:

“Bayan nazari, an dakatar da mambobin da ake zargi gaba daya, har sai an kammala bincike tare da duba sakamakon rahoton abubuwan da kwamitocin da aka kafa suka gano."

Sanusi ya ƙara da cewa tun farko kwamitin ladabtarwa na APC ya fara gudanar da bincike kan zargin cin amana da ake wa tsohon gwamnan mazabarsa da ke karamar hukumar Sagamu.

Sanata Gbenga Daniel.
Hoton Sanata Gbenga Daniel a lokacin da yake gabatar da jawabi a Majalisar Dattawa Hoto: @JustusOGD
Source: Twitter

Ya ce sun yi la'akari da rahoton kwamitin ladantarwa da kwamitin da aka kafa ya yi bincike kafin daukar mataki kan mambobin jam'iyyar guda biyu.

Sai dai awanni kadan bayan haka, mai magana da yawun Sanata Gbenga Daniel ya ce har yanzu ba a turo wata wasika a hukumance kan dakatarwar ba, rahoton TVC News.

APC ta jaddada goyon baya ga Tinubu

Kuna da labarin, jam'iyyar APC reshen Kudu maso Yammacin Najeriya sun jaddada goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Daga zuwa Umrah, hukumomin Saudi sun cafke 'Yar Kano bayan alakanta jakarta da wiwi

Shugabannin jam'iyya mai mulkin Najeriya a shiyyar sun bukaci Tinubu ya sake tsayawa takara karo na biyu a zaben 2027 domin karasa ayyukan alherin da ya dauko.

Shugabannin yankin sun kuma bayyana shirin ɗaukar tallata ayyukan Tinubu a kowace mazaba domin sakon ya kai ga talaka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262