"Ka Ajiye Shettima": An Gayawa Tinubu wanda Ya Fi Dacewa Ya Zama Mataimakinsa a 2027

"Ka Ajiye Shettima": An Gayawa Tinubu wanda Ya Fi Dacewa Ya Zama Mataimakinsa a 2027

  • Kungiyar NENF ta bi sahun masu yin kira ga Shugaba Bola Tinubu kan ya ajiye Kashim Shettima kafin zaben 2027
  • Shugaban kungiyar ya bayyana cewa tikitin Muslim-Muslim.ba zai haifarwa Tinubu da jam'iyyar APC da mai ido ba a zaben gaba
  • Dominic Alancha ya nuna cewa ya kamata Kirista ya zama mataimakin Shugaba Tinubu maimakon ci gaba da tafiya da Shettima

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar Northern Ethnic Nationality Forum (NENF) ta ba da shawara ga Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC kan zaben 2027.

Kungiyar NENF ta yi kira ga Shugaba Tinubu da APC da su yi watsi da duk wani shiri na tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi a zaɓen 2027.

An bukaci Tinubu ya ajiye Shettima
Hotunan Kashim Shettima da Shugaba Bola Tinubu a cikin ofisoshi Hoto: @Stanleynkwocha, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Dakta Dominic Alancha, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

'Ya cancanci tazarce,' An ba ƴan Najeriya dalilai 20 na sake zabar Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar, wadda ke wakiltar fiye da kabilu 200 a Arewacin Najeriya, ta bayyana cewa matsayinta na adawa da tikitin addini ɗaya na APC ya samu amincewar ƙungiyoyin ƙabilu 127.

An bukaci Tinubu ya ajiye Shettima

Kungiyar ta bukaci shugaban kasa ya cire mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takara, ya zaɓi Kirista kafin zaɓen 2027.

Kungiyar ta bayyana cewa tikitin Musulmi da Musulmi na 2023 ya riga ya jawo matsala a dangantakar da ke tsakanin addinai, tare da maida babban ɓangare na al’ummar Kiristoci a kasar nan saniyar ware.

A cewar ƙungiyar, sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa APC na da rauni musamman a jihohin da Kiristoci suka fi rinjaye.

Ta nuna cewa jam’iyyar mai mulki ta sha kashi a jihohin Plateau, Benue, Nasarawa da babban birnin tarayya Abuja, rahoton The Punch ya tabbatar.

Sai dai bayanai sun nuna jam'iyyar APC ce ta yi nasara a Nasarawa a babban zaben na 2023.

Kara karanta wannan

'Kwankwaso ba zai goyi bayan Tinubu a zaben 2027 ba,' Buba Galadima ya kawo dalilai

"Fiye da kaso 80% na Kiristocin Arewa sun ki APC a 2023. Ci gaba da amfani da irin wannan tikitin a 2027 na iya janyo wa jam’iyyar asarar karin jihohi a Arewa ta Tsakiya da wasu sassan Arewa inda Kiristoci ke da karfi wajen kaɗa kuri’a."

- Dominic Alancha

An shawarci Tinubu kan tiktin Muslim/Muslim

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa ko a cikin jam’iyyar APC, akwai shugabannin Kiristoci da dama da suka nuna rashin jin daɗi kan tikitin, wasu ma sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyun adawa.

Ana rade-radin za a sauya Kashim Shettima
Hoton Kashim Shettima a wajen taron FEC Hoto: @stanleynkwocha
Source: Twitter

Haka kuma ta ƙara da cewa sake amfani da tikitin zai iya ƙarfafa haɗin kan jam’iyyun adawa, musamman idan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar jam’iyyar LP Peter Obi, suka kafa kawance.

NENF ta ba da shawarar cewa ya fi APC ta tsayar da Kirista daga Arewa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Ta jaddada cewa haɗin kai da adalci suna da matuƙar muhimmanci a wajen samun nasarar zabe a kasar nan.

Baba-Ahmed: Kuskuren Tinubu game da Shettima

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hakeem Baba-Ahmed ya soki Shugaba Bola Tinubu kan batun sauya Kashim Shettima.

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya yi shiru ba, lokacin da aka rika yada jita-jitar zai sauya mataimakin nasa kafin zaben 2027.

Ya bayyana cewa shirun da Tinubu ya yi, shi ne dalilin da ya sa aka ci gaba da yada-jitar na tsawon lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng