"Ƴan Siyasa Sun Ƙare," Buba Ya ce Ƴan Ci Ku Bamu ke Neman Madafun Iko a Najeriya

"Ƴan Siyasa Sun Ƙare," Buba Ya ce Ƴan Ci Ku Bamu ke Neman Madafun Iko a Najeriya

  • Fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, Buba Galadima ya ce babu sauran nagartattun ‘yan siyasa a Najeriya
  • Ya bayyana kansa a matsayin ɗan siyasa mai fadin gaskiya komai dacinta kuma ko ba a son a ji shi
  • Injiniya Buba Galadima ya bayyana yadda ‘yarsa ta fuskanci wariya saboda dangantaka da shi a gwamnatin baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fiaccen jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa ƴan siyasa masu son kansu ne su ka cika kasar nan.

Injiniya Buba Galadima ya yi wannan bayani ne a lokacin da siyasar ke ɗaukar zafi a gabanin siyasar 2027.

Jigo a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima
Buba Galadima da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Kwankwaso a wani taro Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A hirarsa da Channels Television a ranar Litinin, Buba ya ce shi 'ba ɗan siyasa nagari ba ne,' saboda yana faɗin gaskiya ko da mutane ba sa son jin ta.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ƴan sa kai sun yi wa ƴar bautar ƙasa tsirara, sun lakaɗa mata dukan tsiya

Buba Galadima ya caccaki ƴan siyasa

Daily Post ta ruwaito cewa Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa bai taɓa zama jagora da aka zaɓa ba saboda tsantsar faɗin gaskiya.

A cewarsa:

“Ba a samun ‘yan siyasa a ƙasar nan, abin da ake da su ne masu son kansu ne. Na kira kaina ɗan siyasa mara kyau saboda bana yin karya ko boye gaskiya.”
“Ban taɓa zama kansila ba saboda gaskiya ta."

Buba ya ce ya shafe rayuwarsa gaba ɗaya cikin gwagwarmaya amma bai taɓa rike kujerar siyasa ba, ko ma na kansila, saboda irin dabi’arsa ta faɗin gaskiya kai tsaye.

Yadda ɗiyar Buba Galadima ta shiga matsala

Buba ya ce duk da irin wannan hali na sa, ‘yarsa ta samu nasara a zaɓe, ba ta hanyar adawa ko nadin da gwamnati ke yi ba.

Sai dai ya bayyana cewa har yau ma an hana ta hakkinta na kayan sallama a matsayin tsohuwar kansila, bisa kawai cewa ita ‘yar Buba Galadima ce.

Kara karanta wannan

Gidaje miliyan 2.2 za su samu kudi a sabon shirin tallafin gwamnatin Tinubu

Ya ce:

“’Yata ta zama kansila bayan an zaɓe ta, ba nadin gwamnati ba. Har yanzu ba su ba ta kayan sallama ba saboda ita ‘yata ce. Wannan shi ne halin siyasar Najeriya.”
Jigo a jam'iyyar adawa ta NNPP, Buba Galadima
Buba Galadima a wata hira da kafar yaɗa labarai Hoto: Buba Galadima
Source: Facebook

Jigon na NNPP ya bayyana cewa irin halin faɗin gaskiya ba ya da masauki a siyasar Najeriya.

Gawurtaccen 'dan siyasar ya ce shi mutum ne da idan ka tsaya a gabansa, zai faɗa maka gaskiyar da ba ka son ji.

Buba ya yi nuni da cewa wannan dabi’ar tasa ce ta sa bai samu damar hawa mukamai daban-daban ba duk da shafe shekaru da dama yana fafutukar siyasa a Najeriya.

Buba Galadima ya taɓo shigar Buhari siyasa

A baya, kun ji cewa jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana dalilin da ya sa aka jawo tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari cikin siyasa.

Buba ya ce wata ƙungiya daga Arewa ta lallashi Buhari ya shiga siyasa domin tinkarar barazanar ƙungiyar Oduduwa Peoples Congress (OPC).

A cewarsa, OPC ta mamaye Ilorin a shekarun 1999 da 2000. da nufin rushe tsarin Fulani a yankin, lamarin da Arewa ta ɗauka a matsayin barazana sosai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng